Takarar gwamna: Sha`aban Sharada bai dace ba –Gwagwarwa

Bala Muhammad Gwagwarwa

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

An bayyana dan takarar neman kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin jam`iyyar ADP, Sha`aban Ibrahim Sharada a matsayin wanda bai cancanta ba da ya zama jagora a gari kamar Kano in ji Gwagwarwa.

Jawabi ya fito daga bakin tsohon ma`ajin jam`iyyar APC na kasa kuma dan ta karar gwamnan jihar Kano a karkashin jam`iyyar SDP, Alhaji Bala Muhammad Gwagwarwa a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron kungiyar kakakin Dala wanda aka gudanar a gidan Malam Aminu Kano da ke Gwammaja (Mambayya) makon da ya gabata.

Ya ce, tabbas Sha`aban Sharada na bukatar gogewa da jajircewa a harkar siyasa da kuma sanin makama.

Gwagwarwa ya kara da cewa, tafiyar Sha`aban Sharada tafiya ce wadda bata da makoma a siyasance da kuma hangen nesa domin Sha`aban Sharada Yaron dan siyasa ne da ke bukatar ilimi da karatun siyasa domin Sha`aban Sharada ya fito neman takarar kujerar gwamna amma bai shirya ba.

Hakika kowane irin abu akwai iliminsa da kuma kararun sa domin haka ba a fara gini daga sama dole sai faru daga kasa.

Alhaji Bala Gwagwarwa ya ci gaba da cewa, rashin cancantar ‘yan takarar gwamna da ke jihar Kano ya sanya ya fito kuma idan har ya zama gwamna zai kawo canji mai ma`ana ga al’ummar Kano.

Ya ce, jihar Kano jiha mai matukar muhimmanci amma abin mamakin ta sauka daga kan layi da aka santa musamman kan kasuwanci da sauran harkokin ci gaban al’umma.

Dan takarar ya ce, idan jama`a suka kada masa kuri`arsu za su canja siyasar jihar Kano inda ya kara da cewa, jam`iyar SDP ta kammala shirye-shiryen cin zabe a jihar Kano, domin lokaci ya yi da al’ummar jihar Kano za su yi wa kansu adalci.

Alhaji Bala Gwagwarwa al’umma jihar Kano da kasa baki daya ya kamata su fahinta cewa, SDP ba sabuwar jam`iyya ba ce, tsohuwar jam`iyya ce wanda a ita ce aka zabe shi ya zama shugaban karamar hukumar Nassarawa a shekarun baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *