Talauci, Barazana ga Rayuwar Al’ umma –Munzali

Tura wannan Sakon

Labarai Daga Musa Diso

Wani mai son ci gaban al’umma Alhaji Hamza Munzali Sani ya bayyana talauci da rashin aikin yi ga matasa maza da mata a matsayin wata babbar barazana ga rayuwar al’umma da kuma tattalin arzikin qasa baki daya.

 Ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar ALBISHIR a babban birnin Kano a makon da ya wuce.

Ya ce, ba shakka duk qasar da take fama da talauci da rashin aikin yi ga matasa tabbas za ka ga zaman lafiya da kwanciyar hankali ya yi karanci da kuma rashin sanin makoma.

Ya ce, Nijeriya qasa ce da Allah ya yi wa baiwa ta fanni daban-daban musamman albarkatun kasa da sauransu, amma rashin ingantaccen shugabanci ya sa abubuwa sai koma baya suke yi kullum farashin kayayyaki gaba yake yi da rashin tsaro da tsadar rayuwa da makamantansu.

Sani ya yi kira ga ‘yan Nigeriya da a koma ga Allah da kuma ci gaba da addu’a domin samun sauqin al’amuran rayuwa na yau da kullum. Ya qara da cewa, tsoran Allah da kamanta gaskiya da adalci shi ne mataki na farko da ya kamata jama’a su rike domin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *