Talban Panshekara ya yi furuci kan rayuwar karkara

Talban Panshekara, Alhaji Isyaku Yahaya

Talban Panshekara, Alhaji Isyaku Yahaya

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad S Ahmad

Daya cikin iyayen kasa a jihar Kano, Talban Panshekara, Alhaji Isyaku Yahaya ya ja hankalin gwamnati da masu hannu da shuni kan su mayar da hankali wajen tallafa wa rayuwar mutanen da ke damfame a kauyuka domin suma su zama cikin walwala kamar yadda na birni suke.

Talban ya bayyana hakan ne ga manema labarai a birnin Kano cikin sakon sa na barka da Sallah ga al’ummar Musulmi,wanda kuma ya yi fatan su kammala bukukuwan Sallah lafiya.

Haka kuma Alhaji Isyaku ya kara da cewa, abin takaici ne yadda yake keta yankunan karkara yake ganin mutanenta na fama da matsalar ruwan Talban Panshekara ya yi furuci kan rayuwar karkara Talban Panshekara sha da rashin hanyoyin sufuri da gyare-gyaren makarantu da kuma rashin Malamai, a saboda haka ya nemi gwamnatin kan ta ci gaba da kokarin da take na ganin ta magance matsalar baki daya.

Da ya koma kan rayuwar matasa kuwa, Talban Panshekara ya koka kan yadda rayuwar su kullum take kara gurbata ta hanyar ta’ammali da miyagun kwayoyi da fadan daba da kwacen waya da sauran miyagun ayyuka, a dangane da hakan ya bukace su da gyara halayen su tare da zama jakadun al’umma nagari ta yadda za’a rinka alfahari da su a koda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *