Tallafi ga masu rauni: Jama’a, a yi koyi da Kwamred Tajoudeen Bashir Baba -Iliyasu Ishak

Tallafi ga masu rauni: Jama’a, a yi koyi da Kwamred Tajoudeen Bashir Baba -Iliyasu Ishak
Tura wannan Sakon

Labari Rabiu Sunusi daga Katsina

An bukaci al’ummar jihar Kano da su yi koyi da dan kishin kasa da jama’a, Kwamred Tajoudeen Bashir Baba a iya gudanar da rayuwarsa domin taimaka wa masu karamin karfi.

Hakan ya fito ne daga bakin Iliyasu Ishak yayin gudanar da taron ta ya Kwamred Tajoudeen Bashir Baba murnar cika shekaru 55 da haihuwa a .

Kazalika, Iliyasu wanda shi ne uban taron ya bayyana cewa, lallai Kwamred mutum ne mai son taimaka wa al’umma ta hanyoyi daban-daban ne da ba su kirguwa ko lissafuwa.

Sannan ya kara da cewa, lallai bawan Allah yana taimaka wa wajen harkokin ilimi na mata tare da taimaka wa matasa da marayu da sauran masu karamin karfi tsawon lokaci.

Sannan ya kuma kara tabbatar da cewa, lallai Kwamred ya yi fice wajen taimaka wa al’umma sannan yana da sha’awar ya ga yara mata sun samu ilimi mai zurfi tare da taimaka wa masu wajen bunkasa rayu warsu. Ita ma daya daga cikin yaransa da ya haifa, Malam Surayya Tajoudeen Bashir Baba, ta ce, lallai mahaifinsu ya dora su kan hanyar da za su fahimci mahimmanci ilimi.

Kazalika Surayya ta tabbatar da cewa, ba wai dan tana ‘yarsa ba to lallai yana daya daga cikin mutanen da al’umma ya kamata su yi koyi da halayya irin tashi ta san gina al’umma da sama masu hanyoyin dogaro da kai.

Ita ma uwargidan Tajoudeen Bashir ta ce, lallai maigidanta abin koyi ne ga jama’ar Arewa ba ma jihar Kano ba kadai, domin kuwa ya zuwa yanzu maigidanta ya assasa kungiyoyi fiye da goma domin taimakon al’umma.

Da suke jawabai dabandaban yayin taron manyan baki da suka halarci wurin taron karramawar irinsu wakilin mataimakin gwamnan jihar Kano, Dokta Nasiru Yusif Gawuna da ya samu wakilcin mai ba shi shawar kan harkokin mulki, Dokta Mustapha Yusif Gawuna ya yaba da irin namijn kokarin da Kwamred Tajoudeen Bashir Baba yake yi.

Dokta Mustapha Yusif Gawuna ya kuma bayyana mahimmancin bai wa ‘ya’ya mata ilimi tare da amfani da shi tun daga haihuwa har ya zuwa lokacin da yara za su kasance baligai har ma su zama a dakunan mazajensu.

Shi ma tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Kabir Panshekara da ya wakilci danmajalisar Kumbotso ya bayyana namijn kokarin da Kwamred Tajoudeen Bashir Baba yake yi a matsayin wanda ba gwamnati ba.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa Shehin Malami Ibrahim Khalil ya yi tambihi ga amfanin ilimin mata a mahangar Musulunci tare da hanyoyin da ya kamata iyaye su sa kula wajen bai wa ya’ya mata ilimi.

An dai gudanar da taron cikin hankali da lumana tare da ci dasha dakuma nishadantarwa ga mahalarta taro, inda jama’a da yawa suka bayyana irin kwazo da kokarin Kwamred Tajoudeen Bashir Baba wajen taimakon da yake bai wa marassa karfi tare da fatan zai kara kaimi wajen ci gaba da abin da ya sa a gaba na alheri, sannan sun yi masa fatan alheri da murnar cika shekaru 55 masu albarka tare da fatan Allah ya karo masu albarka a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top