Tallafin karatu: Abba Ganduje ya shirya kawo dauki -Hayin Hago

Tura wannan Sakon

Labarai daga Jabiru Hassan

Daraktan hulda da ‘yan jarida na kwamitin yakin neman zaben Injiniya Abba Ganduje, Malam Kabiru Inuwa Hayin Hago ya bayyana cewa, dan takarar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC na mazabar tarayya ta Dawakin Tofa da Tofa da kuma Rimin Gado, Injiniya Abba Ganduje zai bayar da tallafin karatu ga daliban yankin.

Hayin Hago ya sanar da hakan cikin wata takardar da ya sanyawa hannu kuma ya rarrabawa manema labarai a Kano, inda sanarwar ta bayyana kokarin a matsayin tallafin bunkasa ilimi domin samun rayuwa mai tsari da albarka.

Sanarwar ta kara da cewa, za a bayar da tallafin ga daliban da suka kasance a makarantu daban-daban, kuma babu maganar nuna bambancin siyasa ko na ra’ayi muddin dai dalibi ya fito daga mazabar Dawakin Tofa da Tofa da kuma Rimin Gado.

Malam Kabiru Inuwa Hayin Hago ya kuma jaddada cewa, Injiniya Abba Ganduje zai kasance alheri ga al’ummar mazabar mai kananan hukumomi guda 3, duba da yadda da tsare-tsare da kuma manufofi kyawawa a tsari irin na dimukuradiyya.

Daga karshe, daraktan ‘yan jaridun na kwamitin yakin neman zaben Injiniya Abba Ganduje ya jaddada godiyar al’ummar kananan hukumomin Dawakin Tofa da Tofa da kuma Rimin Gado, bisa kaunar da suke nunawa dan takarar duba da yadda suke da kyakykyawan zato na cewa, zai jawo sauyi a mazabar mai tsohon tarihi a siyasar jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *