Tankiya: APC ta Marafa ta ja kunnen ta Matawalle

Senator Marafa
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Tawagar APC ta kasa ta gargadi mai magana da yawun jam’iyyar APC, bangaren gwamna Bello Matawalle, Yusuf Idris da ya kame harshensa ya daina kebanta al’amura a kan shugabansu na kasa, Alhaji Bello Bakyausuwa wanda ya kasance mai magana da yawun bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa.
Gargadin yana yana cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyoyin, Bashar K Lado, inda ya kara da cewa, Bakyasuwa ya yi aiki a wurare da dama kuma ya jajirce wajen kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya da dama, wanda ya cancanci a yi masa jinjina da mutuntawa daga irin su Yusuf.
Ya kara da cewa, “duk da cewa, ba zai zama da muhimmanci a yi musayar kalmomi ba, amma mun ga ya dace mu bar Yusuf ya fahimci hakan”. Bello Soja Bakyasuwa ba ‘yan aji daya ba ne, ya ce, “mun yi imanin Yusuf bai kasance a ko’ina ba, ma’ana bai san inda yake ba lokacin da shugabanmu ya yi wa jihar Zamfara da Nijeriya aiki”.
A cewar Bashar K Lado ba abin mamaki ba ne idan irin Yusuf da har yanzu bai fahimci siyasa ba, ya fito yana dambarwa da badam badam da hasashensa. Ya ce, tsokaci kan martanin da Sanata Kabiru Garba Marafa ya yi a kan zargin da ake yi wa Janar Ali Gusau, ya ce, an yi shi ne bisa adalci ga kowa da kowa kuma ba yakin neman zabe ba ne. A martanin da ya mayar a Daga shafi na farko Wannan yarinyya bata ta yi, a taimaka mana da cigiya. Sunanta Fatsima.
A Naibawa ‘Yan Lemo gidansu yake. Ga lambar mahifinta Abubakar Mustapha 08067213986. lokacin da ya koma kan “yan bangaren Marafa, Mista Yusuf ya yi magana kan kasancewar shugabanmu a lokacin kaddamar da motoci. Bakyausuwa yana can amma, tambaya shi ne ya rarraba abin da ake kira Ban’s? Ko kuma shi ne ya kai wa ‘yan fashin Daji? wannan batun na Yusuf ya kamata ya fayyace wa al’ummar jihar Zamfara maimakon kai hari kan shugabanmu.
Sakataren ya ce, “Don girman Allah in tambayi Yusuf, Ali Gusau gwamna ne lokacin da aka gano motocin da gwamnati ta bayar daga ‘yan bindiga a jihar Zamfara, ko kuwa shi gwamna ne a lokacin da ake sace mutane 100 ana yi masu fade, ana kashe su. Kungiyoyin dai sun dage cewa, Sanata Marafa yana nan a jam’iyyar APC a matsayin na gaskiya kuma shi ma ba shi da wani shiri na ficewa daga jam’iyyar.