Tarihin sababbin shugabannin sojojin Nijeriya, a taqaice

Shugaban qasa, Muhammadu Buhari ya sanar da nada sababbin shugabannin sojoji.
Janar Leo Irabor aka nada babban hafsan tsaro; Janar I. Attahiru a matsayin babban hafsan sojojin kasa.
Rear Admiral A.Z Gambo aka nada babban hafsan sojojin ruwa sai Iya-bayis Mashal I.O Alao a matsayin babban hafsan sojan sama.
Janar Attahiru dan asalin jihar Kaduna shi ne ya maye gurbin Yusuf Tukur buratai.
Kafin nada shi mukamin, Manjo Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82.
Ya tava jagorantar yaqi da kungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga mukamin bayan wadansu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai inda aka kashe mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.
Da ma Buratai ya ba shi wa’adin kamo shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a mace ko a raye.
Manjo Janar Leo Irabor wanda Buhari ya nada babban hafsan tsaro ya tava rike muqamin kwamandan Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaqi da qungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin Nijeriya.
Daga nan ne kuma Irabor ya zama babban kwamanda na Rundunar hadin gwiwa ta qasashen tafkin Chadi da ke fama da matsalar Boko Haram watau Nijeriya da Nijar da Kamaru da Benin da Chadi.
Air-Vice Marshal I.O Amao – Babban hafsan sojan sama
Air-Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao sabon babban hafsan sojan sama ya maye gurbin Air Marshal Sadique Abubakar ne.
Babban jami’in sojan na sama ya samu horon sojan sama a qasashe Indiya da Sin da kuma Pakistan.
Rear Admiral A.Z Gambo – Babban hafsan sojan ruwa
Air-Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao sabon babban hafsan sojan sama ya maye gurbin Air Marshal Sadique Abubakar ne.
Babban jami’in sojan na sama ya samu horon sojan sama a qasashe India da Sin da kuma Pakistan.
Rear Admiral A.Z Gambo – Babban hafsan sojan ruwa
Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo kafin naxa shi babban hafsan sojan ruwa, kwararre ne a aikin tsaron ruwa da leqen asiri.
Dan asalin jihar Nasarawa ne a yankin Arewa ta tsakiya. Babban jami’in ya samu horon aikin sojan ruwa a Jaji da Afirka ta Kudu.