Taro kan gyara kundin tsarin mulki: Lalong ya furta ra’ayinsa

Taro kan gyara kundin tsarin mulki: Lalong ya furta ra’ayinsa

Gwamna Lalong

Tura wannan Sakon

Daga Mohammed Ahmed Baba Jos

Ina mai matukar farin cikin da marhabin da sanataci masu wakiltar tarayya Nijeriya, zuwa jihar Filato domin saura­ron koke-koken yankin Arewa ta tsakiya, game da sauya tsarin mulkin Nijeriya na 1999, wanda aka gudanar a Jos, ina so na san­ya jagorancin.

Majalisar dokoki ta tara musamman masu kishin kasa domin aikinsu mai muhimmaci, har ma mun karbi taron Arewa ta tsakiya an girmama mu domin ci gaba,

Da taka muhimiyyar rawa a tafiyar dimukuradiyya ta kasar­mu mai girma.

Sanatoci da bakin da aka gayyata mun taru a nan domin yin wani aiki, wanda ba sabon abu ba ne ga ‘yan Nijeriya, musamman domin dawowar dimukuradiyya Nijeriya a1999, yayin da aka yi kokari a baya domin sauya kun­din tsarin mulki daidai da ra’ayin jama a,

Da za’a cim ma duk da duki­yar da aka kashe da kuma lokacin da aka sadaukar, muna fata cewa, taron ba zai tafi da hanzarin wad­anda suka gaza magance wadan­su muhimman batutuwan da suka shafi shugabancin kasa, ta wata hanya ba.

Har ma da barazanar tsaro da hadin kan kasa duk da yake ba daidai ba ne a zargi dukkan ka­lubalan kasa a kan kundin tsarin mulki, amma ya ya muhimmacin hada karfi da karfe game da kun­din tsarin mulki na yanzu, wanda ya hadamu guri daya.

Idan har lokacin da ake ci gaba da wanzuwar lamarin na sa­mun yabo watakila shi ne lokaci da za a gwada wani abu daban, zuwa jin wannan ra’ayoyin yana da matukar muhimmaci, yayin da ake gabatar da wata dama ga wadansu kungiyoyi.

Masu sha’awar gabatar da ra’ayoyinsu game da yadda ake son ganin an gudanar da su a Nijeriya, saboda haka an ba su dandalin domin gabatar da baya­nai game da abinda suka lura da shi daga shekarar 1999 a tsarin mulki, domin saka shi ga mai sha’awar tsahon shekarun da muka yi muna jin zargin bayanai kan yadda tsarin mulki na 1999 ya kasance mai tasiri, ko kuma ya isa wajen magance muhim­man batutuwan kasa yayin da wadansu daga cikin.

Wadannan magangaganu na iya zama kari na daftari tare da nufin inganta shi, manyan baki sun yi halartaci taron da kuma bayanai a gurin taron, sanatocin da suka hallartaci taron sun hada da shugaban taron, SanataAbdul­lahi Adamu da dukkan sanatoci guda tara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *