Taron Maulidi: Garin Unguwar Malamai Al’umma ya yi cikar-kwari

Tura wannan Sakon

Isa  A.  Adamu, Daga Zariya

A ranar littinin da ta gabata al’ummar garin Unguwar Malamai da ke Dutsen – Abba a karamar hukumar Zaariya sun jagoranci taron Mauludi da suka saba shirya wa a duk shekara a gidan Sarkin Unguwar Malamai, inda malamai daga sassan ciki da kuma wajen Zariya, musamman malamai sun halarta.

A lokacin wannan taron mauludi karo na talatin da shida, fitattun malaman addinin musulunci sun gabatar da wa’azin da ke dauke da tarihin Manzon Allah Annabi Muhammadu [ S.A.W. ] da kuma yadda manzon tsira ya gudanar da rayuwarsa da ya shfi mu’amalrsa da hakurinsa da shugabancin da ya yi da dai sauran bayyanai da suka shafi yadda ya zauna da wadanda ba musulmi.

Alhaji Salihu Habibu shi ne Sarkin Unguwar Malamai da aka gudanar taron Mauludin a garinsa, da farko ya nuna matukar jin dadinsa ga yadda a duk shekara ake gudanar da wannan mauludi a gidansa, ya ce, dole kuma ya jinjina wa malaman da suke amsa goron gayyan da ake ba su, domin gabatar da karatu da kuma wa’azi a wajen wannan mauludi.

Sarki Alhaji Salihu Habibu ya kuma yi amfani da wannan damar da ya samu, inda ya yi kira ga al’umma da suke halartar taron mauludin das u tabbatar sun yi amfani da damar karatun da suka samu, musamman yadda shugaban halitta ya gudanar da rayuwarsa da kuma yadda ya sa adalci da hakuri a shugabancin da ya yi.

A zantawarsa da wakilinmu, Alhaji Aliyu Abubakar, shugaban al’umma a wannan gari na Unguwar Malamai, shi yaba wa matasan wannan gari ya yi, na yadda suke halartar taron mauludin, da kuma yadda suke amfani da ilimin da suka samu, a lokacin taron mauludin daga bakin malaman da suke halartar taron mauludin.

Da kuma ya juya ga ‘yan kwamitin da suke shirya taron mauludin, Alhaji Aliyu Abubakar ya yaba ma sun a yadda suke gayyato malamai da suke yin karatu a wajen taron mauludin, sai kuma ya yi kira ga ‘yan kwamitin, da su kara tashi tsaye, na ganin sun ci gaba da gayyato fitattun malamai zuwa wannan taron mauludi.

 A dai lokacin wannan taron mauludi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *