Tashin farashi: Kaiwa kololuwa da dalar Amirka ta yi -Atagi

Alhaji Sagir Yusuf Usman Atagi
Daga Wakilinmu
Har yanzu farashin Dala na ci gaba da kawo tsaiko ga harkokin kasuwanci a jihar Kano dama kasa baki daya, wanda hakan bincike ya nuna shi ya sa farashin kaya a kasuwanni ke kara hauhawa, za ka sayi kaya yau a kasuwa idan ka koma gobe sai ka iske an kara masa farashi.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin babban manajan daraktan Atagi General Enterprices da ke kasuwar Kantin kwari da ke Kano, Alhaji Sagir Yusuf Usman, a lokacin da yake zanatawa da manema labarai a kan yadda farashin Dalar yake kara hauhawa.
Sakir Yusuf Usman, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da cewa, ta sanya ido sosai ‘yan-kasuwar musayar kudaden waje watau masu canji saboda ita gwamnati ta ba su a kan Dala 400 da wani abu su kuma suke sayarwa ‘yan-kasuwa fiye da Naira 500.
Har ila yau ita hukumarEFCC ta rika shiga kasuwanni domin sanin halin da ake ciki na tsadar Dala, ya bayar da misali kwanakin da suka fara shiga kasuwanni har farashin ta ya yi sosai .
Ya ce, matukar gwamnati ba ta takawa abin birki ba, to za’a ci gaba da fuskantar tsadar kaya a manya da kananan kasuwanin da ke fadin Nijeriya, wanda mai karamin karfi shi abin zai fi shafa.
Malam Sagir Yusuf Usman Atagi , duk da halin da ake ciki yana da kyau yankasuwa su ci gaba da rangwantawa masu karamin karfi kamar yadda suka yi a lokacin watan Azumin Ramadan da ya gabata, musamman idan sun zo gurinsu kasuwanci.
Daga karshe, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan babban Sallah da fatan za’a gudanar da Sallah lafiya ya ba mu alherin da ke cikinta