Tashin hankali a Kano: Za mu sanya kafar wando daya da kowa -CP Gumel

CP - Gumel
Daga Rabiu Sanusi Kano
Rundunar ‘yansandan jihar Kano karkashin kwamishina, CP Muhammad Usaini Gumel ta tabbatar da cewa, ba za ta lamunci dukkan wani nau’i na kawo tashin hankali ko tarzoma a bikin rantsar da gwamnan jihar Kano a ranar 29 ga Mayu ba.
Bayanin na zuwa a wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa ya rarraba wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.
Sanarwa ta ce, kwamishinan ya kuma ja kunnen dukkan magoya bayan jam’iyyu da iyayen gidansu kan batun tsatsauran ra’ayi na siyasa domin su janye wannan mummunar akidar ta su.
CP Usaini Mohammed Gumel ya kuma kara da cewa, dukkan masu niyyar yi wa jihar Kano zagon kasa da su kokarta janye wannan ra’ayi nasu. Usaini Gumel a cikin sanarwar ya ce, gaba da cewa, za su ci gaba da gudanar da aiki a dunkule da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da kwanciyar hankali da kare kadarorin jama’a da gwamnati tare da ganin an samu nasarar gudanar da bikin rantsar da gwamnan jihar Kano mai jiran gado da sauran ‘yan majalisar jiha da wakilai cikin koshin lafiya.
“Mun lura da gudanar da bikin rantsar da gwamnan wani abu ne mai tarin muhimmanci da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar dan dorewar tsarin siyasar mu a matsayin kasa daya al’umma daya, domin haka ita ma rundunar ‘yan sanda ta ce, tana da hakkin kare dimukuradiyya da bin diddigin tsarin mulkin kasa.”
Sanarwa ta ce, kwamishinan ya ci gaba da bayyana dokar kasa da tsarin mulki ya ba ‘yan sandan kasa damar tabbatar da ingantaccen tsaro kamar yadda suka yi a lokacin zabe. Domin haka ne ma ya ce, yana ganin hakan ya haifar da zababbun ‘yan takara da kuma bayar da goyon baya ga bikin rantsar da su cikin nasara.
Daga karshe, ya bayar da tabbacin gudanar da aikin babu sani babu sabo kuma dukkan wanda ya tsaya a kan hanyar mu za mu kawar da shi, kuma mu gurfanar da shi a gaban kotu domin kare martabar kasar nan da ingantaccen tsarin siyasa mai dorewa a kasar mu.