Tsadar man fetur a Ikko, Abuja – IPMAN ta fede biri…

Daga Mahmud Gambo Sani
Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta dora alhakin karancin man a Ikko da Abuja da sauran jihohi kan tsadar farashin musayar Dala da Naira da kuma yadda kamfanin kula da alabarkatun mai na NNPC ya gaza sakin wadataccen man.
Akwai dogayen layukan ababen hawa a sassan Ikko da Abuja duk da cewa, ana sayar da lita guda a kan farashin Naira 180 ko ma fiye da haka. Matsalar karancin man ta tilasta wa direbobin motocin haya tsawwala kudin mota ga fasinjoji.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar IPMAN, Cif Ukadike Chinedu ya ce, manyan jiragen ruwa na shigo da man fetur cikin Nijeriya ta kan iyakar Ikko, ya yin da kananan jiragen ruwa ke kai man zuwa tashoshin jiragen ruwa na Ikko da Warri da Fatakwal da sauransu.
A cewarsa, hatta kananan jiragen ruwan, ana biyan su da Dalar Amirka. Jami’in ya bayyana cewa, mawuyaci ne masu gidajen man su sayar da shi a kan Naira 145 kowacce lita a daidai lokacin da farashin hayar jirgin ruwan ya karu daga Dala dubu 38 zuwa Dala dubu 108.