Tsadar rayuwa: An kure wa talaka maleji- Kwamred Mamunu

Kwamred Mamu

Kwamred Mamuni Takai

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Harkar tsadar Gas ta rikita rayuwar ‘yan Nijeriya ba kawai ga masu sana’ar motocin Tifa ko takwarorinsu masu motocin haya.

A sakamakon tsada da tashin gwauron zabi da gas ya yi wanda a baya ana sayen lita a kan N220 yau ana saye fiye da N800.

Shugaban kungiyar masu Tifa da fasa duwatsu na kasa reshen jihar Kano, Kwamared Mamunu Ibrahim Takai ya bayyana hakan

inda ya kara da cewa, sana’arsu a halin da ake ciki suna yi ne kawai saboda kayan ya yi tsananin tsada sabanin abin da ake sayar da shi a baya.

Ya kuma ce, a lokacin da man dizel yake sauki ake sayar da kayan yashi da sauki ana samun riba saboda za ka sayi gas ka je ka sauke kaya a Naira dubu 10 a yanzu kuwa Naira dubu 18.

 Dizel da ake saye Naira 200 shi ne ya koma fiye da Naira 800 idan aka auna za a ga ba domin tsarin kungiyar ‘yan Tifa  ba, da suke kokarin rarrashin mutanensu  da kuma  kallon yanayin al’umma shi ya sa aka sami linzami farashin ya tsaya a kan yadda ake sayen kayan yanzu.

Kwamared Mamunu Ibrahim Takai ya ce, Allah shi ne masani domin yadda ake sayen kayan yanzu talaka ma ba zai iya aiki ba, domin an zo kadamin da talaka an gama kure malejinsa.

Shugaban ya yi kira ga mahukuntan cewa, ya kamata  su kalli halin da al’umma ke ciki a tausaya masu domin  ta kai yanzu komai ya ninka  sai dai fatan Allah ya kawo sauki kan lamarin domin tsananin ya yi tsanani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *