Tsadar taki ba za ta hana noma ba -Umar Abdulhamid

Tsadar taki ba ta hana noma ba
Alhussain daga Kano
Duk da kasancewar tsadar taki ta kai kololuwa, idan aka kwatanta da shekarun baya, hakan ba zai hana manoma su yi noman ba.
Bayanin haka ya fito daga bakin Alhaji Umar A. Abdulhamid, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano.
Abdulhamid, wanda shi neshugaban kamfanin Ahuda Agro and Chemical ya kara da cewa, musabbabin tsadar takin da ake fama da shi a halin yanzu ya afku ne a bisa hauhawar farashin Dalar Amirka da kuma yakin da ake yi a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine da har yanzu ya ki ci ya ki cinyewa, wanda hakan ya sa kasashen duniya suka shiga halin matsi na rashin takin.
Ya ce, kasar Ukraine tana daga cikin kasashen da suke samar da taki mai kyau da kuma inganci, inda ya ce, hatta kamfanonin samar da taki na Nijeriya sun fada matsalar ta rashin taki, musamman na rashin sinadaran da suke sarrafa shibisa matsalar yakin.
Daga bisani ya shawarci manoma da su mayar da hankulansu a kan noman shinkafa da sauran noman kayan abinci, domin kara samun yalwar arziki a kasa. Ya kuma shawarci gwamnatoci da su kara himma wajen taimaka wa manya da matsakaita da kuma kananan manoma domin kara bunkasa noma da kuma wadata kasa da abinci.
Daga karshe, ya yi addu’ar samun damuna mai albarka da kuma yayewar matsalolin da kasar take ciki na rashin tsaro da karayar tattalin arziki da kuma tsadar kayan masarufi.