Tsakanin Almajirai da gwamnatin El-Rufa’i: wace Kofa Kaduna ta bude?

Kaduna ta ciyo bashi har wuya -PDP
Tura wannan Sakon

Dokta Hadiza Nuhu OON

A ranar Laraba 13- 1-2021 cikin dare kamar karfe 12.00 – 12.30, sojoji, yan-sanda da rundunar Kastelea suka isa gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi na Kaduna suka kwashe mutanen gi­dan suka tafi dasu.

Wannan wani yunquri ne na gwamnatin jihar Kaduna don tabbatar da dokar hana barace-barace. Wannan bayani kuwa shugaban rundunar hana barace-barace Major Gen­eral Yahaya Rimi (ritaya) ne yayi bayani da amsa cewa sune suka yi haka ga Almajiran. Major Rimi a wani hira da akayi da shi wacce akayi rohoton ta a jaridar sahelitimes.com ta Alhamis 14-1-2021 ya kara bayani kamar haka. Cewa:

-Yunkuri da sukayi a gidan Shehu farawa su­kayi domin zasu bi duk inda almajirai suke a ja­harsu a kamasu.

-Duk jahohin Arewa sun saka hannu a wan­nan doka ta hana barace-barace

-Ita wannan doka ta basu ikon su kama duk Almajirai su maidasu ja­hohinsu, kasarsu ko su damkasu ga immigration.

Babu matsala idan gwamnati ta dauki mat­aki akan barace-barace amma, ita kanta gwamna­tin meye manufarta na yin haka? Gyara gwamnati ke so tayi har sai ta kama mutum tun bai aikata lai­fin ba? A duk duniya dai an amince cewar mulki ingantacce shi ne wanda yake fahimtar jama’arsa, kawar masu da damuwa irinsu yunwa, tsaro, rash­in aiki da sauransu, ku­santo masu da alheri da samar masu cigaba. Shin gwamnatin mu ta fahim­ci barace-barace daban kuma Almajirci daban? Ba duka Almajirai ke bara ba. Shin gwamnatin mu ta fahimci akwai kundin tsarin mulki na Najeriya (wato constitution) wanda ya bawa kowane mutum ‘yancin zama a ko ina yakeso cikin kasar Najer­iya? Shin gwamnati ta fa­himci cewar mafi yawan barace-barace talauci ne wanda a yanzu yayi kat­utu cikin kasa, rashin ai­kinyi, yan gudun hijira da marayu sun yawaita?

Su fa gwamnati sune aka baiwa hakkin in­ganta rayuwar mutane da al’umma. In yunwa da barace-barace sun yawaita, ya kamata gwam­nati tayi iya kokarinta na dakile hanyoyin damuwa da samar ma mutane ai­kin yi kafin ta hana bara. Musulunci ya kyamaci barace-barace amma, ai bai haramta shi ba. Sabo­da tsananin da muke ciki in an haramta bara to ka bude kofar sace-sace da wasu laifuffukan. Saboda haka, gwamnati mai tau­sayi da adalci sai ta wada­ta mutane da basu kafofin samu, sa’annan ta hana su roke-roke.

Kada mu manta har yanzu Nijeriya bata daddale batun ‘yan shi’a ba. Kuma ga ‘yan boko haram suna ta yaki da jami’an tsaro. Ya kamata gwamnati ta zama mai tausayin na kasa, hangen nesa da toshe kofar fitina.

Almajirci daban, barace-barace daban. Gwamnati tana iya hana bara amma kuma tabi mu­tane cikin gidansu suna bacci a cikin dare da fir­gici ba tare da sunyi bara ba, ta debesu ta rabasu da muhallinsu da iyalansu, ai wannan zalunci ne da shiga hakkinsu da yan­cinsu na zama a duk indasukeso. Hakan da akayi an karya dokar kasa wanda ta hana keta hurumin mutum a gidansa (trespass).

Shi almajirci hakika wata hanyace ta samun ilimi da rayuwa ingantac­ciya kamar yadda na kara­tun boko yake. Almajirci shine tarihinmu da ciga­ban Arewa tun kafin zu­wan turawa. Magabatan­mu sunce mana duk dan Arewa kwakwalwa biyu gareshi,na karatun Alma­jirci da ya iya rubutu da karatu da na boko. Tura­wa Da suka zo arewa, sun same mu mun iya karatu da rubutu da tafi da rayu­wa. Kowane mutum dokar kasa ta bashi yancin yayi duk ilimin da ya ke so ko ya ke buqata.

Hakika tsarin karatun gwamnati na boko da ake­so a rusa almajirci a tura yara can bai ingantaba. Makarantar Gwamnati ta gaza da yaran dake cikin­ta balle ta samu kari.

Saboda haka ya kama­ta mu tambayi gwamnatin Kaduna shin wannan doka ta barace-barace ta juye ta zama dokar haramta kara­tun almajirci da zama gi­dan malamai don koyon karatun Al-Qurani da ili­min addini? Domin dal­iban gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi suna bacci aka debesu ba suna bara aka debesu ba. Hakika ko a fagen yaki, duk wanda ya shagala da bautar Allah bai shiga lamarin kowa ba ya kamata ya tsira.

Sai gashi gwamna­tin Kaduna ta bude qofar tabbatar da hana bara ba wai da kame-kamen masu bara ba. A’a. Da shigacikin gidan mutane suna bacci tana dibansu. Mun soma mulkin kama karya ne? Hakika, in an cigaba da wannan ba’ayi adalci ba kuma shugabanci bai kyautata ba.

Muna kira da babbar murya ga gwamnatin ta­rayya, kungiyoyin addi­nai, kungiyoyin hakkin dan Adam da duk masu ikon tsawatawa dasu dubi Allah su tsaida gwamna­tin Kaduna daga wannan yunkurin hana almajirci maimakon hana barace-barace. Su maida hanka­linsu wurin masu barace-barace kawai ba dalibai a gidan karatunsu ba. Ya jama’a muji tsoron Al­lah don bayason zalunci kuma yana kishin bayinsa da littafinsa Al-Qur’ani. Mu tsaida gwamnatin ka­duna kafin ta kaimu inda bamu fahimta ba. Fitina a kwance take Allah ya la’anci mai tada ita.

Mun fahimci gwamna­ti ta fake da wannan doka ta barace barace ne don ta hana karatun Almajirci da na Alqur’ani. yin haka ya ci karo da shiga yancin rayuwarmu da na addinin­mu, aladarmu da tarihin­mu. Shin wannan kofar zata kaimu ga alheri?

Wadannan dalibai ma­tasa da ake hanasu karatun Alqurani ake tarwatsasu a gidan karatunsu,ina akeso su je? Gidan alfasha ko gi­dan barna? Me gwamnati ta tanadar masu bayan ko­rarsu? hakika gwamnatin kaduna bata fahimta ba.

Ya Allah wanda ya hakicci mulki da mai mulkin, wanda ya halicci dukkan mutane kuma ya tsaida umarnin adalci da gaskia a tsakaninsu ka kawo mana gudummowa mafi alheri cikin wannan lamari na alumma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *