Tsarin adalci, shari’a, sulhu a Arewa-maso-gabas -Masana sun yi taro

Taron Masana na Arewa-maso-gabas
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kungiyar manyan Malaman makarantun shari’a da lauyoyin da manyan sakatarorin din-dindin, hade da wadansu karin masana daga bangarori masu alaka da juna sun hallara a Abuja domin samar da tsarin da ya dace domin samun nasara shirin adalci da sulhu na a Arewa maso gabashin Nijeriya.
A cikin jawabin da ke dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama’a na hukumar kula da hakkin bil-adama ta Nijeriya (NHRC), Hajiya Fatima Agwai Mohammed ke cewa, taron kwararrun dabaru domin habaka tsarin adalci da sulhu yana daya daga cikin ayyukan karkashin wani aiki mai taken “Samar da adalci da sulhu a Adamawa da Borno da Yobe”.
Hukumar kare hakkin dan’adam ta kasa (NHRC) ce ke aiwatar da aikin tare da hadin gwiwa da shirin raya kasashe na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) da suka kuma kungiyar tarayyar Turai (EU).
A jawabinsa sakataren zartarwa na hukumar, Cif Tony Ojukwu (SAN) a lokacin da yake gabatar da jawabin maraba a wajen taron ya ce, hukumar ta yi farin cikin karbar manyan kwararrun masana dangane da bangaren shari’a a jihohin Adamawa Borno da Yobe. Manufar samar da tsarin da ya dace domin adalci na wucin gadi, aikin da muka gabatar wa a wadansu al’ummomi a cikin jihohi uku da ke Arewa maso gabas.
Babban mai ba shi shawara na musamman, Mista Hilary Ogbonna wanda kuma shi ne mai kula da ayyukan ya wakilta a wajen taron, ya bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci a tsara tsarin da zai fi dacewa da al’ummomin da rikicin tawaye ya daidaita” ya jaddada cewa, tsarin ya kamata ya kasance daidai da dabi’u, imani, al’adu da al’adun mutane, wannan zai saukaka.
al’umma su daidaita da junansu,” in ji shi. Ya kuma jaddada cewa, “dole ne a tsara tsarin bisa ka’idojin adalci na dabi’a, sauraron gaskiya, adalcin wadanda aka azabtar da adalcin tsira da daidaito da sauransu.
A nasa jawabin, wakilin hukumar ta UNDP, Mista Elia Bon Rota ya yaba da kokarin hukumar na hada irin wadannan masu tunani wuri guda domin bunkasa tsarin, yana mai cewa, zai ji dadin zama dan kallo a taron.
A nasa sakon fatan alheri, babban sakataren din-din-din kuma lauyan gwamnatin jihar Adamawa Samuel Yaumande Esk, ya ce, shirin shi ne irin sa na farko a yankin Arewa maso Gabas. Ya yi nuni da bukatar samar da ingantaccen tsarin shari’a wanda zai sasanta tare da sake hade kan al’ummomin da suka fuskanci mummunar take hakkin dan’adam sakamakon tayar da kayar baya a yankin. Ya bayar da shawarar cewa, a cikin tsara tsarin, ya zama dole a yi la’akari da bukatun wadanda abin ya shafa domin ba su damar tsinkayar rayuwarsu tare da ci gaba”.
Hakazalika, takwararsa ta jihar Yobe, Hajiya Kadija Alkali ta ce, shirin ba zai zo a lokaci mai kyau ba fiye da yanzu, saboda yawaitar mika wuya na ‘yan tayar da kayar baya da su je kan yi a kullum.
Ta ce, akwai bukatar kowa ya rungumi tsarin adalci da sulhu da ake yi domin yana ba da fatan samun zaman lafiya a tsakanin al’umma”. Hajiya Khadija ta yi kira ga kwararrun da su yi namijin kokari wajen ganin an samar da cikakken tsarin da zai zama jagora domin samun dauwamammen zaman lafiya a yankin baki daya.
Wakilin babban sakatare kuma mai shigar da kara na jihar Borno wanda kuma shi ne darakta mai kula da kararrakin jama’a, BM Bukar Esk ya ce, tsarin adalci da muke dauka daga turawan Ingila ya sabawa al’adarmu, domin haka bai dace da mu ba”.
Ya bayyana shi a matsayin “dogaron da ba dole ba ne kuma mai ban sha’awa ga mutanenmu, ba abu ne mai sauki a tilasta al’adun kasashen waje a kan mutanenmu ba”. A cewarsa, wannan hanya ta adalci da sulhuntawa ta wucin gadi ita ce mafi kyawun abin da zai iya faruwa a wannan yanki ta fuskar samar da zaman lafiya da sulhu kuma dole ne mu tabbatar da cewa yana aiki”.
A wajen taron akwai Malamai daga jami’o’i dabandaban da kuma kungiyoyin fararen hula da ko’odinetocin hukumar na jihohi.