Tsaro a Kano: Kwamishinan ‘yan-sanda ya ziyarci kwamandan ‘yan-sintiri

Isma’ila Shu’aibu Dikko,

Tura wannan Sakon

Daga Alhussain Kano

Kwamishinan ‘yan-sandan jihar Kano, Isma’ila Shu’aibu Dikko, ya ziyarci kwamandan ‘yan-sintiri na jihar Kano, a qarqashin jagorancin Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u a ofishinsa da ke unguwar Hotoro, Kano.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar, Kwamandan ‘yan-sintirin ya nuna farin ciki da ziyarar da kwamishinan ‘yan-sandan ya kawo masu.

Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u ya nuna yadda yake jindaxin aiki da kwamishinan ‘yan-sandan jihar Kano, saboda haka tsakaninsu da Isma’ila Shu’aibu Dikko sai godiya domin babu cin amana, sun ba shi tabbacin cewa, za su ci gaba da ba shi haxin kai da goyon baya wajen samar da tsaro a fadin jihar Kano domin kawar da vata-gari. Wani abin farin ciki ga kwamishinan ‘yan-sandan shi ne, watanni kaxan da kama aiki a jihar, ya sami nasarar kawar da miyagun laifuffuka kashi 80 cikin 100 a jihar.

Shugaban ‘yan-sintirin ya yi amfani da wannan dama game da yadda ake ci gaba da samun zaman lafiya a jihar, wannan ya sa al’ummar waxansu jihohin ke kwararowa jihar.

Gwamnan jihar da kwamishinan qananan hukumomi da DG Abubakar Malami sun bayar da kulawa sosai wajen samar da tsaro a jihar Kano duk mai hankali da tunani zai tabbatar da hakan.

Kwamandan ya ce, lokaci zuwa lokaci ya kan tunatar da ‘yan-sintiri da ke faxin jihar da su zamanto masu gaskiya da amana a lokacin da suke gudanar da aikin samar da tsaro sannan kuma su kiyaye doka da oda .

Ya zuwa yanzu akwai ‘yan sitiri a fadin jihar Kano fiye da dubu 70.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *