Tsaro a Shika: Sheikh Dahiru Bauchi ya yi horon a rungumi addu’a

Isa A. Adamu Daga Zariya
Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Shekh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga al’ummar musulmi da su rungumi yin addu’o’I da ci gaba da tsarkake zuciya da kuma ayyuka nagari da Allah ya yadda da su,domin kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar Nijeriya, musamman wasu jihohi da suke arewa.
Shekh Dariru Usman Bauchi ya bayar a wannan shawarar ce a sakonsa wajen taron Maulidin Annabi Muhammadu [ S.A.W.], da ya gudana a garin Shika da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Shekh Dahiru Bauchi da Sayyadi Mansur Dahiru Bauchi ya wakilce shi ya ci gaba da cewar, babu shakka, rungumar addu’o’I da kuma gyara zukata ga al’umma su ne abubuwa biyu da suka zama wajibi al’umma su ci gaba da yi, domin kawo karshen matsalolin da suke addabar al’umma, musamman matsalar tsaro.
Ya kara da cewar, duk wanda ke lura da yadda gwamnatin tarayya ke aiwatar da wasu ayyuka da suka shafi tsaro, ya san ta na bakin kokarin ta na kawo karshen wannan matsala da za a iya cewar, babu sako da lungunan da wannan matsala ta tsaro ba ta leka ba.
Amm duk da haka, Sayyadi Mansur ya ce matsala ta tsaro da za a iya cewar ta kawo nakasu ga bangarori da dama da suka hada da rasa rayukan al’umma da hana noman kayayyakin abinci da dai matsaloli ma su yawan gaske da suka yadu a sassan Nijeriya, musamman a jihohin arewa. A game da zaben shekara ta 2023 da uku kuma, Shehin malamin yay i kira ga dukkannin al’ummar da suka isa yin zabe da su bi dokar hukumare zabe na samun katin zaben da ta tanda, domin zaben ‘yan siyasar da suke bukatar wakiltar al’umma a madafun da za a yi zabe a kan su, tare da amfani da hankali wajen zaben mutane nagari da za su fuskanci matsalolin da suke addabar al’umma a yau,a cewarsa tun daga matsalar tsaro da sauran matsalolin da ambata a baya.
A sakonsa wajen taron maulidin Shehi Dahiru Usman Bauchi yay aba wadda ta saba shirya wannan maulidi, wato Sayyada Khadija Ibrahim, da aka fi sanin ta da ‘ayr Zazzau ta Barhama, ya ce ladan da ake samu na shirya maulidi, bai dace ya tsaya ga maza kawai ba, a cewarsa, ya dace mata, su yi koyi da Sayyada Khadija, na shirya maulidin da kuma bayar da duk gudunmuwar da suka dace, domin ciyar da addinin musulunci gaba da kuma samun ladar da babu wanda ya isa ya bayyana yawan ladar da wanda ko wadda ta shirya maulidi ke samu, sai mai kowa – mai komi.
A zantawar da wakilinmu ya yi da Sayyada Khadija Ibrahim, wato ‘yar Zazzau ta Barhama, da farko nuna jin dadin ta na yadda a duk shekara manyan malamai da sauran malamai ke amsa goron da ta ke raba wa, domin halartar wannan maulidi da ta ke jagoranta a duk shekara.
Ta kara da cewar, ta fara shirya taron maulidi a cikin dakinta, ta yadda ta ke dafa abinci, ta rarraba wa al’umma cikin gida, daga nan sai ta fara gayyatar al’ummar musulmi da kuma malamai da suke gabatar da majalisi a kofar gida,ya zuwa wannan shekara da ta ce ta shafe shekara biyar ke nan da fara jagorantar maulidi a kofar gida da al’uuma ke halarta a duk shekara.
Sayyada ta Barhama ta kamala da yaba kwamitocin da ake kafa wa domin gudanar da maulin da kuma godiya ga Shekh Dahiru Usman Bauchi, na yadda a duk shekara ya ke turo daya daga cikin ‘ya’yansa zuwa wannan maulidi da kuma sauran malamai da suke zuwa daga ciki da wajen jihar Kaduna.