Tsaro a Zamfara: Kwamitin kar-ta-kwana ta kama masu sayar da lambobin jabu

Tsaro a Zamfara: Kwamitin kar-ta-kwana ta kama masu sayar da lambobin jabu

Abubakar Dauran

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

A ranar Littinin din da ta gabata ne kwamitin kar-ta-kwana kan matsalar tsaro,wanda ke karkashin jagorancin Abubakar Dauran ta sami nasarar kama wadansu da ake zargin suna sayar da lambobin bogi.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kama su, Abubakar Dauran ya ce, sun sami nasarar kama wani dan kabu-kabu ne wanda ke gudanar da sana’arsa a garin Gwagwalada, bayan sun kama shi ya cika babur dinsa da mai, bayan sun duba jakarsa sai suka sami wasu lambobin bogi.

Ya kara da cewa, shi wanda aka kama ya ce, ya sayi lambobin ne daga wani da ke sayar da babura a ‘yar Dole mai suna Ibrahim, in da ya ce, wani yake kawo masa yana saye daga Kaduna a kan kudi Naira 1200, su kuma suna sayar wa Naira dubu 2 su wadanda za su saya a hannun sa su sayar dubu 2500.

Da yake amsa tambayar ga manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Malam lbrahim Gusau, ya ce, lalle abin da ake zargin suna yi gaskiya ne, kuma daga lokacin da ya fara sana’ar zuwa yanzu ya sayar da fiye da 30.

Ya kara da cewa, daga garin Kaduna ake yi masa, ana kawo masu suna sayar da masu hayar babur, ko wadanda suke neman lambar babur tsohuwa, sai dai ya tabbatar wa manema labarai cewa, lalle sun yi laifi kuma tsautsayi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *