Tsaro a Zamfara: Matawalle ya dakatar da zaben NUJ

Alaka da ‘yan-fashi: Gwamnan Zamfara ya dakatar da sarkin Dansadau

Gwamnan Zamfara Bello Matawale

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Bello Muhammad Matawallen Maradun ta dakatar da zaben ‘ya’yan kungiyar ‘yan jarida ta NUJ na shekarar 2022 da aka shirya, wanda zai gudana a ranar Alhamis da ta gabata, har zuwa wani lokaci saboda rashin tsaro da ke addabar jihar Zamfara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar yada labarai, Barista Sani Nasarawa kuma aka rarrabawa manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

Tun da farko an shirya gudanar da zaben a ranar 14 ga Afrilu, 2022 amma hedkwatar NUJ ta kasa ta maiyar da shi baya saboda wadansu dalilai zuwa ranar 12 ga Mayu, 2022.

A cewar sanarwar, lokacin da aka sanya bai dace ba saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da shi, inda ta kara da cewa, ma’aikatar yada labaran jihar za ta tuntubi jami’an tsaro domin sanya rana da lokacin da ya dace domin gudanar da zaben.

Haka kuma an mika takarda ga shugaban kungiyar ta kasa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da daraktan tsaro na jihar, da kuma kwamandan hukumar tsaro na farin kaya ta kasa reshen jihar Zamfara

. Idan ba a manta ba cikin mako guda an sami yawaitar kai hare-hare cikin wadansu kananan hukumomi inda aka kashe mutane fiye da 60, a yayin da hakan ya sanya gwamnatin jihar ta kai daukin gaggawa na abinci da kudade.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *