Tsaro: Kaura ya jagoranci taron gaggawa

Tsaro: Kaura ya jagoranci taron gaggawa
Jamilu Barau daga Bauchi
A ranar Litinin din data gabata gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kira taron Majalisar Tsaro na gaggawa, bayan rahotannin kwararar mutane zuwa wadansu kananan hukumomi sakamakon matsalar tsaro da ‘yan fashi suka yi a garin Gaidam da ke jihar Yobe.
Bayan taron, sakataren gwamnatin jihar Bauchi ya yi bayani game da sakamakon taron kwamitin tsaro, karin bayanai game da bayanin nasa sun hada da wadannan:
Bayani game da yanayin tsaro a cikin al’ummomin, kan iyaka na kananan hukumomin 4, yawan ‘yan gudun hijirar (IDPS) zuwa cikin Gamawa da karamar hukumar Dambam sakamakon harin na Gaidam.
Gwamnati ta kirkiro da samfuri, domin sa ido da ayyukan tsaro a yankunan kan iyaka.
Gwamnati ta kira taron tsaron domin daukar kwararan matakan da za su tabbatar da tsaron dan kasa, musamman a yankunan kan iyaka na kananan hukumomin Dambam, Zaki, Gamawa da Darazo.
Ya kuma yi tsokaci kan wadansu masu aikata laifuffuka wadanda aka gano sun saci kayan sadarwa a ciki biyar daga cikinsu an kama su kuma ana kan bincike a kansu.
Lura da yanayin sanin gaskiyar cewa, babbar barazana a yanzu ita ce kwararar ‘yan gudun hijira a cikin kananan hukumomin Dambam da Gamawa. Ya ci gaba da sanar da ayyukan agaji na kayan abinci da za a aike wa IDP’s a yankunan da abin ya shafa.