Tsaro: Sai an rungumi addu’o’i, bai wa sarakunana iko -Mai Almajirai

Isa A. Adamu Daga Zariya
An bayyana dawo da tsaron lafiyar al’umma da dukiyoyinsu da kuma sana’ar noma da cewar sai an dawo da sai al’ummomin Nijeriya sun rungumi addu’o’I da kuma dawo da ayyukan sarakuna iyayen al’umma, kamar yadda suke gudanar da ayyukan kafin Nijeriya ta sami ‘yancin kai.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin fitaccen malamin addinin musuluncin nan mai suna Shekh Tanimuddari Mai Almajirai da ke garin Kamfani a gundumar Dutsen Abba ta karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, a lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, kan matsalolin tsaro da a yau za a iya cewar ta zama gagara badau ga gwamnatocin Nijeriya.
Shekh Tanimuddari ya ci gaba da cewar, duk wanda ke lura da al’amurran da suke faruwa da suka shafi tsaro a wasu jihohin arewa, babu ko shakka, a cewarsa, al’umma a dai na addu’o’I, abin da kawai aka fi mayar da hankali a kansa tattauna matsalolin tsaro a dandali da sauran wuraren zaman jama’a, wannan, kamar yadda Shehin Malamin ya ce, babban kuskura ne al’umma ke yi dare da kuma rana.
Ya kar da cewar, babu wata matsala da za ta addabi al’umma, al’ummar su rungumi addu’o’I, su kaance a cikin wannan matsalar, sai dai ba su yi tawasuli da addu’o’in da suke yi bad a kuma kyawawan ayyukansu, a lokaci kadan za su ga mafitan matsalar da suke ciki, musamman, a cewarsa a wannan lokaci da babu matsalar da ta addabi al’umma, sai matsalolin tsaro, da ke zama sanadiyyar rasa rayukan al’umma da kwace ma su dukiyoyinsu da sunan garkuwa da su.
Da kuma ya juya ga yadda a shekarun baya da kowa ya san muhimmancin shugabannin al’umma tun daga ma su Unguwanni ya zuwa sarakunan yanka, birni da kauye sarakuna sun duk wani bako day a sauka gari ko kuma wanda ya sayi gida ko kuma fili, amma a halin yanzu, an aje wadannan bayin Allah a gefe guda, sai matsala ta taso, an rasa yadda za a kawo karshen matsalar, sai a mayar da su ‘yan kwana – kwana, domin samun mafitar matsalar.
A kan haka ne Shekh Tanimuddar Mai Almajrai, ya tunatar da wakilan al’umma da suke majilisun tarayyar Nijeriya, musamman a wannan lolkaci da aka motsa na yin kwaskwarima tsarin mulkin Nijeriya, da duba yiwuwar dawo wad a sarakuna ayyukan tsaro a hannunsu, kamar yadda suke yi a shekarun baya, domin kawo karshen wannan matsala, a cikin dan kankanin lokaci.
A karshen tattaunawar da wakilinmu a Zariya ya yi da wannan fitaccen malami ya kuma yi kira ga shugaban kasa da ya duba shawarwain da ake ba shi na sauke shugabannin rungunonin tsaro, ya duba wannan shawara, domin in ya aiwatar al’ummar Nijeriya na ganin za a iya samun canijn halin kaka – nika yin a kamfar tsaro a wasu jihohin Nijeriya kafatan, musamman jihohin arewa