Tsaro: Sarkin zazzau ya yi umrnin addu’o’in zaman lafiya

Sarkin Zazzau ya koka da ta’annatin ‘yan-ta’adda
Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli yay i kira ga al’uumar masarautarsa da kuma Nijeriya baki daya da su ci gaba da yin addu’o’I, domin kawo karshen matsalolin tsaro musamman garkuwa da mmutane da sauran matsaloli da suka addabi al’umma,ba masarautar Zazzau kawai ba.

Mlam Ahmed Bamalli yay i wannan kira ne a lokacin da yak e gabatar da jawabinsa na ranar karamar sallah a ranar littinin da ta gabata a fadar Zazzau.

Ya ci gaba da cewar, kamar yadda al’umma suka rungumi addu’o’I a watan azumi dare da kuma rana, a cewarsa, bai dace al’umma su aje batun addu’o’I a gefe guda ba, domin, addu’o’I, kamar yadda mai martaba arkin Zazzau ya ce, shi ne babbar mafita ga matsalolin da suke addabar Nijeriya, musamman Nijeriya ta arewa.

A jawabin mai martaba Sarki, ya nuna matukar jin dadinsa ga malamai da suka gabatar da Tafsiri a watan azumi, musamman na yadda ako wace rana sai sunyi addu’o’I na musamman kan matsalolin tsaro da babu sako da lungunan da wannan matsala ba ta leka ba, sai ya ce ya na fatan za su dore da yin addu’o’in kamar yadda suka yi a lokutan tafsiri.

Da kuma mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya juya ga al’umma,musamman na masarautarsa, sai ya yi kira garesu da su ci gaba da darussan da suka koya da kuma wadanda suka aiwatar domin samun mafita daga mai kowa – mai – komi, a cewarsa, su ci gaba da aiwatar da ibada da kuma ayyukan alhairai, domin samun mafita a yau ya zuwa gobe.

Ya kuma kara da cewar, lokaci da al’umma za su fahimci jami’an tsaro ba za su sami nasarar da suke bukata ba, sai al’umma sun ba su hadin kai, musamman na shaida ma su duk wani labarin da zai taimaka ma su, na fitar da bata – gari da suke labewa a cikin al’umma, in al’umma sun yi haka, kamar yadda mai mai martaba ya ce, a dan lokaci kadan matsalolin tsaro za su zama tarihi.

A dai kan batun tsaro, Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Bamalli ya umurci sauran ma su rike da sarauta a masarautar Zazzau da su hada hannu da al’ummomin da suke tare da su, domin gano duk wani bakon – ido da ya shiga wuraren da suke, ta yadda jami’an tsaro za su sami saukin sauke nauyin da aka dora ma su, na tabbatar da tsaro a cikin al’umma.

Da kuma ya juya ga yadda alamun damuna ta fara bayyana, ya yi kira ga manoma da ka da su raina ruwan da za su yi shuka abubuwan da suka saba shukawa, in manoma suka yi shuka da wuri, babu ko shakka, a cewar Mai martaba Sarkin Zazzau, sun sakamakon da mai duka zai ba su, a dalilin hobbasar da suka a lokacin da ruwan damuna ta fara sauka.

A KARSHEN JAWABINSA Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi kira ga ma su Unguwanni da su rika bayyana wa jami’an kiwon lafiya dukbullar cutar da ba su san da it aba, wannan mataki, a cewarsa, zai maukar tasiri, wajen murkushe ko wace irin cuta, kafin ta zama gagara – badau a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top