Tsaro: ‘Yan Nijeriya, a dukufa yin addu’o’i

Tura wannan Sakon

Daga Salihu Gazewa

An yi kira ga al’ummar kasar nan kan su kara him­matuwa wajen rungumar addu’o’i domin samun dau­wamammen zaman lafiya a kasar nan musamman yankunanmu na Arewa da ke fama da mashassharar tsaro.

Dagacikin garin Aujar­awar Alkali da ke karamar hukumar Gezawa, jahar Kano, Alhaji Ahmad yaku­bu Ahmed (Ruwata) ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa.

Dagacin ya ce, babu wani abu da al’ummar kasar nan za su runguma fiye da addu’a domin ita ce maganin kowacce irin musiba.

Ruwata ya ce, babu wata al’umma da za ta ci gaba matukar tana cikin halin rashin kwanciyar hankali,

inda ya ci gaba da cewa, ak­wai bukatar dagewa sosai da addu’a a wannan sabuwar shekarar da muka shiga ta 2022.

Da yake bayani kan shirye-shiryen da gwamna­tin jahar Kano karkashin jagorancin gwamna Gan­duje na bai wa Mai-martaba sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir sandar kama aiki, Ruwata yaba wa gwamna ganduje kan nada shi sarautata, yana mai cewa, lallai Ganduje ya zama mi­kiya mai hangen nesa.

Alhaji Ruwata ya kuma ja hankalin al’umar ma­sarautar ta gaya kan su ru­banya goyon bayansu ga Sarkin na Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir don ya sami karfin giuwar ciyar da masarautar gaba.

Bugu da kari, Alhaji Ruwata ya jaddada godi­yarsa ga mai girma hakimin Gezawa Alhaji Mahmud Aminu Yusuf Mai Unguwar Mandubawa kan yadda yake aiki kafada da kafada da su tare da tsaiwar daka wajen ciyar da yankin na Gezawa gaba.

Ruwata ya ce, babu abin da zai ce da hakimin Gezawa da wakilin haki­min Alhaji Kabiru Tanko da uwa uba fadar Mai martaba sarkin Gaya da kuma dan­dazon masoya da suka zo daga sassa daban-daban na jahar Kano da wasu jahohin makwabtanmu don gudanar da bikin da ya yi a fadarsa ya kuma gode wa talakawansa na kasar Aujarawa kan goy­on bayan da suke bashi, ya kuma mika sakon sabuwar shekara ga al’ummar kasar nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *