Tsige mataimakin gwamna: Tambuwal ya nuna wa ‘yan majalisar Zamfara yatsa

Gwammna Tambuwal

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, ya bayyana cewa, babu wata majalisa da za ta qi aiki da hukuncin kotu, kamar yadda majalisar jihar Zamfara take qoqarin yin wasa da hukuncin kotu a kan shari’ar mataimakin gwamna jihar, Mahadi Aliyu Gusau.

Da yake magana da ‘ya’yan jam’iyar PDP a garin Gusau, Tambuwal wanda ke neman tikitin tsayawa takarar shugaban qasa a jam’iyar PDP ya ce, ya yi mamakin yadda majalisar ke qoqarin sava qa’idar kan lamarin mataimakin gwamna.

Ya qara da cewa “ Babu wata doka a qasar nan ko kuma suna neman nuna jahilci kan aikin, duk da umarnin kotu na tabbatar da matsayinsu amma ana qoqarin yin aiki ba bisa qa’ida ba.”

Tambuwal ya shawarci shugabannin siyasa da su fahimci matsayin jagoranci kuma su mutunta mutum, domin babu wanda zai iya canza qaddara a rayuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa, a shekarar 2015 lokacin da shugaba Buhari ya karvi ragamar mulkin Nijeriya ya fuskanci matsaloli da dama amma maimakon a rage wahalhalu sai lamarin ya fi wanda gwamnatin APC ta gada, a cewarsa, ya kamata a fuskanci matsalar rashin tsaro da duk wani abu mai tsanani.

Tambuwal ya nuna alhininsa kan ayyukan ‘yan bindiga da suka yi sanadiyar kashe waxansu ‘yan jihar Zamfara waxanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wurin taron tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce, lokaci ya yi da za a fara tunkarar shirye-shiryen zaven 2023.

Ya ce, a shekarar 2019 ’yan takara 7 da suka fafata a lokacin da suke neman tikitin takarar zaven shugaban qasa na PDP daga yankin Arewa maso Yamma sun kasance na biyu a quri’u.

Ya qara da cewa, “yan takarar shugaban qasa 5 daga yankin Arewa maso Yamma, muka yanke shawarar sauka daga mulki muka mara wa gwamna Aminu Waziri Tambuwal baya domin neman tikitin tsayawa takarar shugaban qasa a jam’iyar PDP kasan cewarsa matashi ne kuma mai kuzari”, in ji Bafarawa.

Ya kuma nuna damuwar

sa kan ayyukan ‘yan fashi da sace-sace da kashe-kashen mutane da ake fama da shi a jihar Zamfara. Bafarawa ya buqaci al’ummar jihar da su fara gudanar da gagarumar addu’o’i ga shugabanni, su kuma kasance masu jajircewa da kuma hikimar tinkarar qalubale. Shi ma da yake magana mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Mahdi Aliyu Gusau ya buqaci wakilan jam’iyar da su jajirce domin samun nasarar jam’iyyar PDP, ya yi kira ga gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da ya ci gaba da riqe kowa idan ya ci zaven shugaban qasa a shekarar 2023

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *