Tunatarwa a kan Ramadan (II)

Tura wannan Sakon

Daga Zainab Sani Shehu Kiru

Daga shaikh Khalifa Sharif Amin Niasse Badawa Kano Da Sunan Allah, Mai Rahama, mai jinkai, Salatin Allah da amincin sa ga masoyin sa gwargwadon girmansa a wajensa da ahlinsa masu girma.

Bayan haka, ya ku ’yan’uwana masu albarka! Ku sani, watan Ramadan yana daya daga cikin watannin da Musulmi suke haba-haba da zuwansa a cikin watannin Musulunci.

Wata ne da yake cike da alherai masu tarin yawa, wata ne da rahamomin da Allah Yake saukarwa a kan Musulmi suke yawaita.

Domin Musulmi su kara samun rabo daga wadannan alherai da rahamomi, akwai bukatarsu kintsa kansu matuka domin yin maraba da wannan wata, ta yadda za su shiga cikin sa cikin sauki tare da gudanar da ayyukan alheri masu yawa a daukacin watan.

’Yan uwana maza da mata! Yana da kyau Musulmi ya kintsa wa zuwan watan Ramadan tare da shirin aikata dukkan ayyukan kirki da ake so a cikinsa, domin samun alherai da rahamomin da ke cikinsa.

Hudubar mu ta yau, za mu duba muhimmancin watan Ramadan ne da hanyar da Musulmi za su tunkare shi tare da kintsa masa kafin ya iso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top