Uban Doma ya yaba wa sarkin Fika -Saboda adalci

Alhaji Abdusalam
Yahaya Wakili, Daga Damaturu
Uban Doman Hakimin Kara, Alhaji Abdusalam Adamu Mamadi ya yabawa mai martaba sarkin Fika, kuma shugaban majalisan sarakuna na jihar Yobe, Alhaji (Dokta) Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa da Hakimin Kara, Alhaji Baba Maina Gimba ga bisa yadda suke mulkan al’ummansun bisa adalci da gaskiya.
Alhaji Abdusalam Adamu Mamadi ya yi wannan yabo a lokacin da yake zantawa da Albishir a ofishinsa a garin Potiskum.
Ya ce, al’umar masarautan Fika baki daya sun gamsu da mulkin mai martaba sarkin Fika tare dana hakimin cikin garin Potiskum, Alhaji Baba Maina Gimba bisa yadda suke jagorancin al’uman su bisa adalci da gaskiya.
Uban Doman Hakimin Kara ya kara da cewa, duk abin da shugaba yake yi wa al’umarsa na adalci daci gaba mai martaba sarkin Fika da hakimi sun yi wa al’umarsu. Daga nan ya yi adu’a Allah ya kara musu lafiya da martaba.
Ya ci gaba da cewa, mai martaba sarkin Fika da hakimin kara mutane ne masu son suga kowa yaci gaba, kuma mutane masu mulki na adalci sun rungumi kowa da kowa a jikinsu ba waraiya.
Abdusalam Mamadi ya ce, masarautan Fika bata da bambanci ko kadan kowa da kowa natane, kuma ga son baki domin ko daga ina kazo garin Potiskum, masarautan Fika zata karbe ka hanu biyu-biyu.
“Abinda hakimin kara, Alhaji Baba Maina Gimba yayi min har na mutu bazan taba mantawa dashi ba, domin a cikin mutane da yawa ya daukoni ya bani wannan mukami na Uban Doman Kara. Ubangiji Allah ya saka masa da alkairi.’’ In ji Abdusalam Adamu Mamadi.
Uban Doman Hakimin Kara, Alhaji Abdusalam Adamu Mamadi ya ce, Alhaji Baba Maina Gimba dadtijo ne, kuma mutum ne na jama’a babba da yaro kowa nasa ne. Allah ya saka masa da alkairi.
A karshe, ya yi adu’a Allah ya albarkaci masarautan Fika, kuma Allah ya yi masu jagora, Allah ya kara masu lafiya da nisan kwana mu kuma zamu ci gaba da biyayya.