Umarnin zaman gida a jihar Kano, bai shafi makarantu ba -In ji Kwamishinan ilimi

Kwamishinan ilimi
Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Musta­pha Abdullahi

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malan Muhammad Sunusi Sa, id Kiru ya ce, umarnin za­man gida da gwamnatin jihar Kano ta bayar ga ma’aikata bai shafi makarantu ba, inda ya ce, dukkan makarantu za su ci gaba da aikinsu na horas da dalibai yadda ya kamata, Sunusi Kiru ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da manema labarai a ranar Talata da ta gabata

Muhammad Sunusi Sa, id Kiru ya ce, ma’aikatar ilimi za ta samar da duk wadansu kayan kariya da ake bukata ga dalibai da malamai da sau­ran ma’aikata da suke aiki a makarantun saboda a tabbatar da cewa, ana bin duk wani tsari da matakai na kariya saboda da kare kai daga kamuwa da an­nobar korona.

Kiru ya kara da cewa zamu tabbatar da cewa duk makaran­tun da suke a fadin jihar suna bin matakan kariya da jami’an lafiya da hukumomi suka bayar, na kare kai daga korona.

Kiru ya ce, ma’aikatar ilimi za ta samar da wani kwamiti mai karfi a dukkannin shiyo­yin ilimi 14 da ke fadin jihar Kano, wanda aikin kwamitin shi ne taimaka wa hukumar ilimi wajen duba yadda ake tafiyar da horas da dalibai a makarantu, bi sa ga tsarin da hukumomin lafiya suka bayar na kariya daga korona, wanda za su rinka kawo mana rahoton abinda suka ga ni duk mako.

Kiru ya kara da ba da tabbacin cewa, sun tattauna da gwamna Ganduje kan batun ci gaban ilimi a jihar Kano, wanda Gwamna ya ba ni tabbacin cewa duk abun­da ya shafi ilimi zai ci gaba da gudana kamar yadda aka tsara ta hanyar bin matakan kariya, sannan za mu bawa makarantu duk wata kulawa da suke bukata tare da hadin kai.

Mun sa ni cewa, gwana­tin jiha ta ba da umarnin ga ma, aikatan jihar da su zauna a gida, har sai an sanar da ranar dawowar su anan gaba, tare da rufe dukkannin gi­dajen kallo da wajen bikin a fadin jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *