Wakilin Hakimin D/Tofa ya Sha Yabo -Saboda Shugabanci Nagari

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Al’ummar gundumar Dawakin Tofa sun bayyana jin dadin su bisa yadda wakilin hakimin yankin Alhaji Kabiru Ali Dawakin Tofa yake tafiyar da riqon gundumar tare da tabbatar da adalci wajen gudanar da shugabanci a duk lokacin da wani abu ya faru na sasanci.

 Wakilin mu ya sami zantawa da waxansu daga cikin mutanen yankin inda suka bayyana cewa, Alhaji Kabiru Ali ya cancanci a yaba masa duba da yadda yadda qoqari wajen ganin ana zaune lafiya a qaramar hukumar Dawakin Tofa a matsayinsa na wakilin hakimin yankin.

Malam Dauda Muhammad Ali, wani mai riqe da sarautar gargajiya a qasar dagacin Kunnawa ya ce” gaskiya muna jin daxin yadda wakilin hakimin Dawakin, Alhaji Kabiru Ali Dawakin Tofa yake riqe da al’ummar yankin, domin haka muke qara jinjina wa a gareshi bisa wakilci na gari da yake yi tun lokacin da Allah ya ba shi riqon gundumar mu’.

Shi ma a nasa vangaren, Mai unguwar Zangon Dawanau da ke qasar dagacin Dawanau, Malam Bala Adamu ya sanar da cewa wakilcin Alhaji Kabiru Ali ya kawo fahimtar juna da ganin darajar mutane musamman ganin irin qoqarin da yake yi wajen tabbatar da cewa, zaman lafiya yana ci gaba da wanzuwa a yankin.

Sannan ya nunar da cewa, a matsayin su na shugabannin al’umma, sun gamsu da yadda wakilin hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Kabiru Ali yake gudanar da ayyukan sa tare da yin fatan alheri ga hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Ismail Umar Ganduje saboda nasa qoqarin da yake yi wajen bunqasa gundumar tun lokacin da aka naxa shi.

Shugaban makiyayan madatsar ruwan Kunnawa, Ardo Alhai Geza da wani manomi, Malam Sulaiman Umar sun bayyana cewa, wakilin hakimin Dawakin, Alhaji Kabiru Ali ya yi qoqari sosai wajen tabbatar da cewa, babu wata rigima tsakanin makiyayan da manoma a qaramar hukumar Dawakin Tofa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *