Wannan zamani: Jihar Kano, ina muka dosa?

Daga Kwamared Ibrahim Abdu Zango
Jihar Kano an kirkiro ta ne a 1967. A da tana cikin mashahuran birane tun tali-tali, watau, lokacin kasuwancin Sahara. Kano tun shekaru aru-aru babbar alkarya ce wacce dukkan kasashen Arewa, yawancinsu na fararen fata, watau Larabawa na Arewacin Afirika, kamar su Libya da Tunusiya da Algeriya da kuma Moroko.
Duk wadannan kasashen da aka ambata, da burinsu su shigo kasar Kano, domin yin kasuwanci irin na da. Ko da ni da nake da karamin karni na shekaru daga 1958 zuwa 1964, na ga Afzinawa suna kawo kayayyaki kamar Kanwa da Manda da zuma da sauransu, su kuma su zo da kudaden kasashensu ayi musu canji a nan, su shiga Kantin Kwari, domin sayen akoko, wanda ake rina musu su yi kayansa su koma kasashensu, kususan Nijar da Mali, tunda suna sahara sun fi son kaya bakake.
Gaskiya unguwarmu Zango, tana daya daga cikin unguwannin da Buzaye suke sauka da rakumansu har su sami lokaci mai tsawo a gidan mai saukarsu, watau mai unguwa. Ka ga tun wancan lokacin, Kano ta shahara wurin karbar baki tun tale-tale, kuma cikin ikon Allah har gobe da jibi ita ce take rike kowa naka.
Na san dai ba ma ‘yan uwa bakar fata ba, hatta fararen fata a 1940 zuwa 1970 sun sami gurbin kasuwanci, daga nan ne aka sami Kantin Kwari, wadda a da kwarori ne daga Lebanon suka yi dandazo a wurin, kuma yanzu ‘yan kasa yawancinsu daga makotan Kano, kamar Katsinawa wadanda suka dade wurin kasuwanci tun kafin mu zo duniya, haka akwai Sakkwatawa, dukkansu ‘yan uwa ne na jini duk da jihohinmu daban-daban, amma dai shekaru masu yawa ana tare kuma an yi arziki sosai. Kano ta kunshi mutane da yawansu ya kai da wuya a kididdige su cikin kankanin lokaci, amma dai sun fito daga gabas da yamma har da kudancin kasar nan, kuma sun sami zaman lafiya da wadata, ba tare da kuntatawa kowa ba, ko kyashin abin da mutum ya mallaka.
Kano da jama’arta, abu ne mai wahala su sa ido bisa ga abin arziki da wani bako ya mallaka. A takaice, Allah Ya bai wa jama’ar Kano baiwar son baki, kuma babu gori ko kyashi kamar yadda a yanzu wasu wurare ake kyamar baki koda kuwa anan Arewa! Abin da ba a gane ba, duk inda ake kin yaduwar baki za ka ga komai ya tsaya cak, babu albarka.
Dauki birnin tsarki, Madina, za ka sami kowa cikin kaunar kowa, wannan ya faru shekaru fiye da dubu da doriya, kuma ko yau ka je haka abin dai yake babu canji.
Sanin haka ne ya sa, Kanawa da jiharsu ta Kano suka rungumi kowa nasu, kuma an ga arziki ko’ina, kususan daga 2015 zuwa 2022 za ka iske irin ci gaban kasuwanci da gine-gine irin na London da Dubai. Duk da masu kyashi suna tofa yawun kiyayya, domin bakin cikin ba su suka kawo ci gaba ba.
Mai karatu zai ga farkon makala wacce ayar tambaya ce, ganin an sa mutanen Kano a gaba kususan attajiri Aliko Dangote da Akanta Janar na tarayyar Nijeriya wanda ake ta yi masa terere, kawai saboda ana zarginsa da abin da har yanzu zargi ne kawai ba a tabbatar ba, amma ana ta yada karya bisa wannan taliki, shin wannan Akanta na tarayya shi ne ministan kudi ko shi ne gwamnan babban bankin Nijeriya, babu daya, dole a yi bincike kafin batawa wannan dattijon arziki suna, kawai saboda zargi marar madafa, shi kuwa Dangote ana cewa ya karye, a’ina Malam?
Daga Kwamared Ibrahim Abdu Zango, Chairman Kano Unity Forum, Kano, Nigeria. 08175472298