Wasan dambe, al’adar Hausawa tun tale-tale – Sadauki

Wasan dambe, al’adar Hausawa tun tale-tale —Sadauki

Wasan dambe

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Shugaban kungiyar ma su shirya wasan dambe a Nijeriya baki daya mai suna ALHAJI ANAS SADAUKI kuma Madakin Fawan Sabon Ga­rin Zariya kan yadda ya run­gumi bunkasa wasan dambe da dalilan da suka say a mayar da hankalinsa a wan­nan vangare.

Ga dai yadda tattau­nawarmu ta kasance da shi,

— An kwana biyu ba a yi wasan dambe ba a inda aka saba a Sabon garin Zari­ya, ko a kwai wasu dalilan yin hakan ?

Babbar matsalar da ta sa mu ka dan dakata da wasan dambe musamman a nan Sabon garin Zariya, dalilin shi ne matsalar nan da babu inda ba inda ba ta shiga ba a sassan Duniya, wato cutar Korona da ta kunno kai, ta kuma yi illa ga ko wane vangare na rayuwa,ba wasan dambe ba ma kawai, hard a sauran vangarori ka­mar ilimi da kiwon lafiya da nomad a tattalin arziki da dai sauran matsaloli ma su yawan gake.

Wannan matsala, ita ce babbar matsalar da ta kawo ma na tsaiko a wasan dambe da mu ka saba yi shekaru da dama da suka wuce a nan karamar hukumar Sabon gari da kuma sauran garuru­wa da suke sassan Nijeriya, ba arewacin Nijeriya kawai ba, kuma wannan matsala ce ta korona da ta kunno kai komi ya tsaya ma na a wasan dambe baki daya.

— A kwai wasu lokuta da karamar hukumar Sabon gari ta dakatar da ku daga shirya wasan Dambe, ina aka tsaya zuwa yau ?

Babu ko shakka dalilin matsalar cutar Korona ce ya sa aka dakatar da mu, kamar yadda aka dakatar da ko wane abu a Nijeriya da du­niya baki daya, ba karamar hukumar Sabon gari kawai ba.Da matsalar wannan cuta da aka ambata aka ba mu damar ci gaba da shirya wasan dambe kamar yadda mu ka saba shekaru da dama da suka gabata.

—- Daga wasu garuruwa da kuma jihohi ku ke samun ‘yan damben da ku ke hulda da su ?

Lallai mu na samun ‘yan dambe daga jihohi ma su yawan gaske, wanda ba sai na bayyana sub a, amma duk da haka, mun fi samu daga jihohin arewa goma sha tara.

—-Alhaji Anas an dade ana son jin tab akin ka na dalilan da suka sa ka run­gumi wasan dambe shekaru da dama da suka gabata, ko za mu ji dalilan ?

To, ka yi babbar tam­baya, a gaskiya amsoshin su na da yawa, amma dalili na farko shi ne na farko dai ina son wannan wasa, a matsayi na cikakken ba hausa gaba da baya kuma sama da kasa, sai kuma dalili na biyu shi ne kafin in fara tunanin run­gumar wasan dambe, na yi dogon bincike da ya shafi al’adun ba haushe, sai na fa­himci mafiya yawan al’adun hausawa su na kushewa, tun daga na kida da waka da dai sauran al’adu ma su yawan gaske, kan haka ne sai na fa­himci, rungumar farfado da wasan dambe shi ne ma fi sauki a waje na, abin da na fara ke nan, zuwa yau da mu ke tattaunawa da kai.

—-Za mu iya cewar, ka fara gamsuwa da yadda ka sa wannan kuduri na far­fado da wasan dambe ?

Babu ko shakka na sami nasarar da ban tava tunanin zan samu ba, domin ka dubi gidan dambe da ke Sabon garin Zariya a jihar Kadu­na, a duk ranar da ake yin wasan damben yadda jinsin mutane ke halartar gidan, abin na ba ni mamaki, do­min duk wani da ake tunani mai sana’a ko ma’aikacin gwamnati ko dan kasuwa ko mai dammara da kuma saran ma’aikata su na zuwa wannan gida a duk rana, wannan ne nuna ma ni ce­war, al’ummarmu hausawa sun gamsu da yunkurin da na yi, ni kuma ina matukar jin dadi fiye da tunanin mai karanta wannan tattaunawa da mu ke yi.

—Wani tsari ake yi wa wadanda suka fito daga wasu jihohi na wajen kwan­ansu da sauran bukatunsu ?

Ai kafin ma su kasance a wannan gari, mu na zama da su, mu bayyana ma su tsare – tsaren da mu ka yi ma su, da ya shafi wajen kwanansu da lafiyarsu da dai duk abin das u ke buka­ta a matsayinsu na bak­inmu, saboda haka, babu wani dan dambe da za mu gayyata ya sami wata mat­sala, ba mu warware ma sa ba, in ma dan dambe ya kawo kansa, ba tare da mun gayyace shi ba,mu na run­gumarsa da hannu biyu da kuma yi ma sa duk abin da ya kamata na matsayinsa na bakonmu.

—– Wace alaka wan­nan kungiya ta ke da shi da sarakunan arewacin Nijeri­ya, wanda za mu iya cewar, a kwai dan gugguvin al’adu a wajen sarakunan ?

Mu na kyakkyawar alaka da sarakuna, domin zan iya tuna wa mai mar­taba Sarkin Zazzau Mari­gayi Alhaji Shehu Idris, mun tava kai ma sa ziyara, ya kuma sa ma na albarka da kuma ba mu duk goyon bayan da suka dace, wan­nan ne ya sa, kafin rasu­warsa a duk babbar sallah mu ke zuwa fdar Zazzau mu na gudanar da wasan dambe kamar yadda mu ke yi a gidan dambe, amma a nan fadar, duk wanda ya je kyauta zau kalli damben, kuma mun yi haka ne do­min alakarmu da marigayi Sarkin Zazzau Alhaji She­hu Idris, kuma nan da ‘yan kwanaki za a yi bikin bab­bar Sallah, kammala shirya wasan damen a fdar Zazzau kamar yadda mu ka saba.

—-Baya ga gidan dambe da ke Sabon garin Zariya, a kwai wasu garuruwa da ka ke jagorantar wsan damben?

Lallai a kwai garuwa da mu fara gudanar da wasan damben kamar Sakkwato da Katsina da kuma Ikko, wato Legas duk mu na da gidajen dambe a garuruwa da jiho­hin da na ambata, kuma za mu ci gaba da bude wa a nan ba da jimawa ba, kuma duk garuruwan da na bayyana ma ku, ina da wakilai da na dora ma su alhaki gudanar da wasan, kuma su na bakin kokarinsu na amanar da na dora ma su.

—Ya batun tsaro a gi­dajen damben da ka bayya­na ma na ?

Ai ba mu da wata mat­sala a batun tsaro, domin duk inda za mu bude gidan damben, mu na shaida wa jinsin jami’an tsaro, kuma su na zuwa gidajen daga lo­kaci – zuwa – lokaci, kuma kamar yadda na bayyana a baya, cikin jinsin mutanen da suke kallon dambe a duk rana jami’an tsaro na vangarori da daman a ciki, saboda haka, mu na da cikakken tsaro fiye da tunanin mai tunanin tsaro a gidajen dambenmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *