Wasannin nakasassu na kasa: Kano ta ci gaba da yin mamaya

Wasannin nakasassu
Labari Salisu Baso, Daga Abuja
A ranar Litinin 11 ga Afrilu, aka fara gasar wasanni ta kasa ta masu bukata ta musamman watau nakasassu karo na farko a Nijeriya.
Jihar Kano ta fara gasar da kafar dama bayan da ta sami lambobin zinare da azurfa da tagulla kimanin 20.
‘Yan wasan nakasassu masalle-tsalle da suka hada da Lawan Bashir da Safiyanu Abdullahi Ibrahim da Shu’aibu Abdullahi Isma’il su
ka sami lambobin zinare da azurfa da tagulla a gasar.
A wasan kwallon kafa na nakasassu (Para soccer) kuwa, Kano ta tashi wasa 1-1 da jihar Filato, bayan da dan wasa Abdullahi Muhammad (Ortega ), ya rama wa Kano a zagaye na biyu na wasan da aka kai ruwarana tsakanin jihohin biyu.
Hakazalika, dan wasan Kano na wasan kwallon tebur watau (Para table tennis), Gbenga Osinawo, ya sami galaba a kan dan wasan jihar Kwara, Mustapha Alanamo, da ci 11 da 4 da 11 da 5 sai 11 da 3, inda ya bayar da jumullar 3 – 0. `
A bangare daya ‘yan wasan na Kano na ci gaba da fafata wasanni daban-daban a gasar da suka hada da, wasan tseran ruwa (Swimming), sai kwallon kafa ta kurame (Deaf soccer) da sauran wasannin motsa jiki na (Athletics), a gasar da aka shiga rana ta biyu, bayan kaddamarwa a babban filin wasa na Moshood Abiola, da ke birnin tarayya, Abuja