WHO ta ja damarar yaki da zukar sigari

Tura wannan Sakon

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta qaddamar da gangamin yaqi da shan taba sigari na shekarar 2021, inda ta wallafa sakonni a kafofin sadarwar zamani da ke bayyana dalilai 100 na guje wa ta’ammali da sigarin.

Annobar korona ta sanya miliyoyin masu shan taba sigari sun bayyana aniyarsu ta rabuwa da ita, lamarin da ya sa gangamin zai karkata ga taimaka wa mutane miliyan 100 wajen yin watsi da dabi’ar shan sigarin.

Shirin na Hukumar Lafiya ta Duniya zai samar da kyakkyawan yanayi ga masu buqatar barin shan tabar ta hanyar samar da ingantattun manunfofin yaqi da mu’amala da sigarin tare da wayar da kan al’umma a game da dabarun da kamfanonin tabar ke amfani da su domin rinjayar jama’a.

Hukumar Lafiya ta Duniya tare da qawayenta za ta samar da wani dandali a kafar intanet, inda dimbim al’umma za su samu bayanai masu amfani da za su kai su ga yin watsi da shan sigari a cikin harsuna da dama da suka hada da Ingilishi da Faransanci Sinanci da Larabci da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *