Xavi ya ci kofinsa na farko a Barcelona

Tura wannan Sakon


Xavi ya lashe kofinsa na farko a matsayinsa na kocin Barcelona bayan ya doke Real Madrid a wasan karshe na kofin Spanish Super Cup.

A wasan da aka buga a Saudiyya, Xavi mai shekaru 18 ne ya fara zura kwallon farko kafin Robert Lewandowski ya ci kwallo ta biyu.

Pedri ne ya ci wa Barcelona kwallo ta uku kafin Karim Benzema ya farkewa Real kwallo daya. Barcelona ce ta fi haskakawa a wasan a yayin da Real Madrid na shiga cikin yanayi mara dadi a tsawon lokaci na wasan.

A yanzu haka Barcelona ce a saman teburin gasar La Liga inda ta baiwa Real tazarar maki uku. Wannan shi ne wasa na takwas da kungiyoyin biyu suka kara a Spanish Super Cup, inda Real ta yi nasara a shida wato a (1988, 1990, 1993, 1997, 2012 da kuma 2017) Ita kuwa Barcelona ta lashe a 2011 a wasan karshe da ta fuskanci Real a kofin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *