Yakar kalaman batanci ya zama dole

Tura wannan Sakon


Daga Muhammad Hamisu Abdullahi

Yana da muhimmancin gaske yin tsokaci a kan wannan gagarimin batu, ganin cewa ana cikin kakar siyasa, inda gari ke ta dumama sakamakon yakin neman zabe, da ‘yan siyasa da suka fito daga jam’iyyun kasar nan, ke yi.

A kowacce rana ta allah, tun daga lokacin da hukumar zabe ta kasa, watau inec, ta sahale wa jam’iyyun cewa su baza yakin neman zabe, ake ta samun wanzuwar wasu kalamai na batanci daga bakunan ‘yansiyasa, inda su ka bazama wajen yin batanci ga daidaiku ko kuma gamayyar mutane.

Watau yadda batun ya ke, shi ne cewa wasu gungun ‘yantakara ko kuma daidaikun su, an sawo su a gaba, domin a karya mu su kwarin gwiwar ci gaba da zage dantse a fafutukar su ta wajen cimma burin su.

Misali, a nan kano, za a fahimci al’amura da dama, kuma daga cikin su akwai wadanda suka shafi furta kalaman batanci, ma su cuturwa, musamman ta hanyar yin amfani da kafafen yada labarai, musamman gidajen rediyon da allah ya albarkaci jihar da su, inda wasu marasa kishin mutunta dan’adam su ke cin karen su ba babbaka, su ke yin batanci ga ‘yantakaran wasu jamiyyun adawa dan biyan bukatun iyayen gidansu, dan a sami na kaiwa bakin salati.

Kamar yadda batun ya ke, akwai kafafen yada labarai da dama a cikin wannan jihar ta kano, inda kusan dukkan su ba sa karkata akalar su wajen rage ko dakile barazanar da ke wanzuwa daga kalaman batanci.

A a, kai ka ce dada ruruta wutar su ke. Amma a nan ya kamata hukumar kula da ingancin aikin gidan rediyo da talbijin, watau nbc ta dinga tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro.

Watau ya kamata ta dauki matakin horo mai tsanani akan ire-iren wadannan kafafen yada labaru domin kaucewa illolin wadannan kalamai a cikin al’umma.

Har’ila’iyau, daya daga cikin hikimomin samar da jamiyyu da yawa a kasa irin tamu ta nijeriya, ita ce dan a ba ‘yan kasar zabi da yanci wajen shiga daya daga cikin su, sakamakon manufofin da ta ke da su, domin bada gudun mawa wajen gina kasa, amma ba su zama gwadaben batanci ga juna ba.

Ya kamata a sami tsari mai kyau na mutunta juna akan doron siyasar kasarnan ko wannan jiha tamu ta kano.

Ya kamata a yi yakin neman zabe a cikin tsafta da tsari mai kyau.

Al’ummar kasarnan, musamman na nan jihar kano, dole su hankalta ta wajen yin la’akari da illolin da ke tattare da kalaman batanci domin su na haifar da tashin-tashina da daukar karan tsana.

Idan aka yi la’akari, za a fahimci cewa kalaman batanci kamar dada karuwa su ke a cikin al’ummar duniya, kuma sababbin kafafen sadarwa na zamani su na taka rawa sosai na tabarbar al’amura, dole ne su canza akalar su su daina yada irin wadannan kalamai.

Domin an yi nazari cewa su wadannan kalamai na batanci su ne ummul abaisin yin barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Dadin dadawa, saboda muhimmanci da wanzar da zaman lafiya ya ke da shi ne da kuma nuna kyama ga kalaman batanci a doron duniyar nan ne ya sa majilisar dinkin duniya, watau un, ta ga dacewar kebe wata rana don a dakile kalaman batanci a duniya baki daya.

Saboda haka, ya zama dole ayi la’akari da haka wajen kare mutuncin dan’adam da dokokin wanzar da zaman lafiya.

Al’ummar wannan kasa ko kuma jihar nan tamu, ya zama dole a gare su da jajirce wajen yakar daukar karan tsana da nuna banbanci a tsakanin su.

Duk ‘yan’uwan juna ne. Yakamata kowa da kowa a nuna kyama ga kalaman batanci soboda illolin da su ke tattare da su.

Dukda ya ke kalaman batanci sun dan dade da wanzuwa, amma a yan kwanakinnan su na neman su zama ruwan dare gama duniya a inda su ke wanzuwa kusan kullun.

Abin bakin ciki shi ne, sudai wadannan kalaman batanci, ba wait kawai illar su ta tsaya kacokan ne a matakin daidaikun jama’a ba ne, a a wata hanya ce ta kai farmaki ga al’umma baki daya. Mutane da dama sun yi daidaito akan cewa lallai kalaman batanci su na haifar da babbar illa ba wai kawai ga tunanin dan’adam ko kwakwalwar sa ba ne ba, harma illa ta zahiri ya ke da ita da zaran wata fitina ko rikici ya barke. Ma su iya magana sun ce aiki da lura ya fi aiki da hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *