Yakin neman zabe: Gobe, Dambatta za ta karbi Gawuna/Garo

Dambatta za ta karbi Gawuna/Garo
Daga Jabiru Hassan
A gobe za a gudanar da taron kaddamar da kungiyar yakin neman zaben ‘yan takarar APC ta mata karkashin jagorancin dattijuwa Hajiya Alpha Dambatta wadda aka fi sani da maman maja.
Kungiyar wadda ta sha alwashin shiga lunguna da kauyukan kananan hukumomin Dambatta da Makoda ta kafu ne da aniyar yin aiki tukuru domin ganin dukkanin mutanen da suka tsaya takara a tutar jam’iyyar APC sun sami nasara a matakai daban-daban na madafar iko a zaben shekarar 2023.
Bugu da kari, kungiyar za ta gudanar da yakin neman zaben domin takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin da na majalisar wakilai, Injiniya Hamisu Chidari da na jiha da kuma dan takarar gwamna da mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo a dukkanin mazabu 21 da ke kananan hukumomin Dambatta da Makoda cikin yardar Allah.
Da take karin haske kan kungiyar, Hajiya Alpha Dambatta maman Maja ta ce, sun kafa kungiyar domin rama alheri da alheri duba da yadda uwargidan gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta taimaki al’umma musamman matan jihar Kano.
Sannan ta sanar da cewa, a matsayinta ta jagorar tafiyar kungiyar, za ta yi aiki sosai domin tabbatar da cewa, dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar APC sun lashe zaben su ba tare da tsaiko ba, inda kuma ta yaba wa matan Dambatta da Makoda da ke mazabu 21 saboda goyon bayan da suke yi wa jam’iyyar APC.
A nasa ran cewa, uwargidan gwamnan jihar za ta kasance babbar bakuwa a wajen taro tare da tawagar matan jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki da ke kananan hukumomin guda biyu.