‘Yan-bangar siyasa sun fada tarkon jami’an tsaro -A ZamfarA

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu ibrahim Gusau

A kokarin da gwamnatin Zamfara take yi na kauwar da matasa masu bangar siyasa a fadin jihar, kwamitin yaki da ‘yan-daba karkashin Bello Bakyasuwa ta kama fiye da ‘yanbangar siyasa 60 tun bayan fara harkokin siyasa gabanin zaben 2023.

Shugaban kwamitin Bello Mohammed Bakyasuwa ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau babban birnin jihar.

A cewarsa, kwamitin ya kama wadansu ‘yan siyasa ciki har da tsohon ministan yada labarai, Alhaji Ikra Aliyu Bilbis da sakataren karamar hukumar Tsafe da sauransu wadanda ake zargi da daukar nauyin ‘yan-daba.

Ya kara da cewa, wadansu daga cikin wadanda ake zargi da daukar nauyin ‘yan bangar siyasar wadanda suka ari takalmin kare, kuma a cewarsa suna nan suna neman su ruwa a jallo domin daukar matakin da ya dace.

Bakyasuwa ya yi nuni da cewa, an mika dukkan ‘yan-bangar siyasa da aka kama fiye da mutane 60 ga hukumomin da suka dace domin fuskantar hukunci.

A cewarsa, kwamitin yaki da ‘yandaba da ke karkashinsa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an dakile duk wani nau’in ‘yan-daba da shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran abubuwan da ke da alaka dasu domin a samu zaman lafiya a jihar.

Ya kuma bayyana cewa, tuni gwamnatin jihar ta amince da daukar karin jami’an yaki da ‘yan-daba dubu 2 da nufin taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da miyagun laifuffuka a jihar.

Ya ce, “mun karbi takardun masu neman aiki fiye da 6700 daga cikinsu, za mu dauki 2000 aiki, sai 1000 wadanda za su yi aikin sa kai, bayan samun nasarar horar da su kamar yadda gwamnatin jihar ta amince”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *