‘Yan-bindiga sun farmaki Sarkin Birnin Gwari

Yan bindiga sun kai hari kan jerin gwanon motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibiril Mai Gwari II.
Rahotanni a Najeriya na cewa, an kai wa Sarkin hari ne a kan hanyarsa ta zuwa Birnin-Gwari a maraicen ranar Talata.
Wadanda suka shaida faruwar lamarin sun ce Sarkin ba ya ko daya daga cikin motocin da aka hara.
Direban motar Sarkin Umar Jibril ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, ‘yan bindiga rike da bindigogi sun rika jefo rassan bishiya kan titi domin tilasta masu tsayawa.
“Ba mu tsaya ba, Sun ta kokarin harbi na, wani hasashi ta wuce ta saman kaina.”
Ya ce, banda ciwon da gilashi ya ji musu babu wanda ya ji wani rauni.
Karamar hukumar Birnin Gwari daya ce daga cikin kananan hukumomin Jihar Kaduna da ake yawan kai hare-haren ta’addanci cikinta.