‘Yan bindiga sun sace sarkin Bungudu

‘Yan bindiga sun sace sarkin Bungudu

‘Yan bindiga sun sace sarkin Bungudu

Tura wannan Sakon

Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Fulanin Bungudu, da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya, mai martaba Alhaji Hassan Attahiru.

‘Yan bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda daya daga cikin ‘ya’yansa da kuma basaraken masarautar Zannan Bungudu Alhaji Abdulmalik Zubairu ya tabbatarwa BBC.

Bayanai sun ce an kashe daya daga cikin jami’in ‘yan sanda a musayar wutar da ‘yan bindigar suka yi jami’an tsaron da ke tare da sarkin cikin mota a hanyar Abuja. Sarkin yana cikin sarakunan Zamfara masu daraja ta daya. Babu dai wata sanarwa daga rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, yankin da al’amarin ya faru.

Sace sarkin wani babban kalubale ne musamman a daidai lokacin da aka dauki mataki na toshe layukan sadarwa da hana cin kasuwannin mako domin maganin ‘yan bindiga masu kai hare-hare- da satar mutane.

“Muna tare da shi jiya a Abuja, ya tafi Gusau kuma yana kan hanyar shi ta dawo wa daga Kaduna aka kira mu aka ce an sace shi,” in ji daya daga cikin manyan ‘ya’yansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *