‘Yan jarida, a bi dokokin aikin jarida -Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau ya koka da ta’annatin ‘yan-ta’adda

Sarkin Zazzau Bamali

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya hawarci ‘yan jarida da suke gudanar da aikinsu a shiyya ta daya a jihar Kaduna, da su tsayuwa irin na maid aka, wajen bin dokokin aikin jarida sau – da – kafa, a duk lokacin da suka tashi rubuta ko wane irin labara da al’umma za su ji ko kuma za su gani.

Sarkin Zazzau ya bayar da wannan shawarar ce a lokacin da sabbin shugabannin kungiyar ‘yan jarida da suke gudanar da ayyukansu a shiyya ta daya suka kai ma sa ziyarar ban girma da kuma neman albarka daga bakin mai martaba Sakin Zazzau Malam Ahmed Bamalli.

Da farko sarkin ya nuna matukar jin dadinsa na yadda sabbin shugabannin bisa jagorancin sabon shugaban kungiyar Malam Sagir Muhammad Auwa, y ace ya na fatan hakan zai dore a tsakanin masarautar da wannan kungiya ta ‘yan jarida.

A game da yadda ‘yan jarida ‘yan jarida ke gudanar da ayyukansu a fadar Zazzau kuwa, mai martaba Sarki ya ce dole ya sa wa ‘yan jarida albarka, a dalilin da ako wane lokaci, gidajen rediyo da kuma tallabin, duk rana, sai an bayyana wasu muhimman labarai daga fadar Zazzau.

A dai jawabin mai martaba sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya kuma nanata kira ga ‘yan jarida da su kara tsabtace ayyukansu, ta yadda yadda za a banbance aya da tsakuwa, a tsanin ‘yan jarida da ma su amfani da kafafen watsa labarai na zamani, a cewar mai martaba Sarkin Zazzau, bas u da tsarin gudanar da rubuce – rubucensu.

Tun farko a jawabinsa, sabon shugaban da aka zaba, Malam Sagir Muhammad Auwal, ya shaida wa mai martaba sarki cewar,sabbin shugabannin da kuma mambobin kungiyar sun kasance a fadar Zazzau ne, domin neman albarkan sarki da kuma tabbatar ma sa da matsayin mabban uba ga wannan kungiya ta ‘yan jarida a shiyya ta daya, Malam Sagir ya kuma bayyana wa mai martaba sarki cewar, a kwai tsare – tsare da nan ba da jima wa ba, za a shirya wasu tarurruka da mai martaba sarkin Zazzau zai kasance uba ga wanna taro.

A karshen jawabinsa ya bukaci mai martaba sarki da ya duba matsalolin da wannan kungiya ke fukanta, ta yadda zai dauki matakan warware matsalolin a ciikn lokaci, ba tare da an daga kara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *