‘Yan-kasuwar Ibrahim Taiwo na neman tallafin gwamnati -Bashir Magaji

‘Yan-kasuwar Ibrahim Taiwo na neman tallafin gwamnati -Bashir Magaji

‘Yan-kasuwar Ibrahim Taiwo

Tura wannan Sakon

Daga Alhussain Kano

Yan-kasuwar da ke kan titin Ibrahim Tayo a Kano na neman tallafin gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna, Dokta Umar Abdullahi Ganduje, kamar yadda yake taimaka wa kungiyoyin da ke jihar.

Babban tallafin da suke bukata shi ne yake yashe masu magudana ruwa da kullum yake addabarsu, wanda hakan ke matukar barazana ga ‘yan-kasuwar da ke wurin.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin daya daga cikin shugabannin kungiyar kasuwar, Alhaji Bashir Magaji Musa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Alhaji Bashir Magaji Musa, wanda har ila yau shi ne mai kantin sayar da kaya na Marhaba General Enterprices ya ce, wadansu lokutan ‘yan-kasuwar ne suke hada kudi domin yashe magudanar ruwan yanzu abin ya fi karfinsu sai gwamnatin jiha ta shigo, sannan kuma suna fama da rashin wurin ajiye motoci musamman ga bakin ‘yan-kasuwa.

Bashir Magaji Musa ya yi amfani da wannan dama da nuna farin cikin sa a kan yadda kungiyar ta su take bunkasa da kuma ci gaba a karkashin shugaban kungiyar, Alhaji Jafar musamman yadda ake samun hadin kai tsakanin ‘yan-kungiyar da kuma yadda aka samu nasarar tara ‘yan-kasuwar wuri daya maimakon a ce suna rarrabe.

Ya kuma tabbatar da cewa, kasuwar tana da tsaro sukan kuma kai rahoton wani abu wanda ba su amince da shi ba ga hukumomin tsaro.

Ya ce, kungiyar tana da mambobi fiye da 200 suna kuma bin dokokin kungiyar sai ya roke su da su ci gaba da mara wa shugabannin kungiyar baya da kuma hadin kai domin duk inda aka samu hadin kai, babu shakka za a samu ci gaban da ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *