‘Yan Nijeriya, a zabi Atiku Abubakar -Mubarak Musa

Tallafa wa ‘yan Kwari: Sagir ya jinjina wa Atiku Abubakar

Tallafa wa ‘yan Kwari: Sagir ya jinjina wa Atiku Abubakar

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Wani shararren dan siyasa kuma daya daga cikin cordinator na takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, jam’iyar APC ta gaza kuma lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su canja tunaninsu domin ganin an kawar da gwamnatin Buhari daga kan mulki a kakar zabe ta 2023.

Furucin ya fito ne daga bakin Mubarak Musa a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin Kano a satin da gabata ya ce, APC karkashin shugabancin Muhammad Buhari ta gaza, do min haka akwai bukatar a canja gwamnati a 2023.

Musa ya ce, rashin tsaro da rashin aikin yi ga matasa da rushewar tattalin arzikin kasa ya zama babban kalubale ga al’ummar Nijeriya saboda haka mafita a nan shi ne, a zabi jajirtacce kuma gogaggen dan siyasa wanda zai fitar da ‘yan Nijeriya daga cikin kangin wahalar rayuwa da talauci da rashin tsaro.

Mubarak ya ce, hakika babban kalubale ne wanda kawai zai iya kawar da matsala shi ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar domin shi jajirtacce ne wanda yake da karamar gwamnati a hannu shekara da shekaru idan Allah ya sa aka zabe shi dorawa kawai zai yi.

Mubarak ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da kada su yi kuskure irin na 2015 da 2019 wajen zaben shugabanni marasa kishi wanda babu jama’a a gabansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *