‘Yan Nijeriya, a zabi Tinubu ya zama shugaban kasa -Aisha Abdussamad

Tinubu

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

An yi Kira ga ‘yan Nijeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu da su zabi Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar APC domin yin haka alheri ne da kuma ci gaban al’ummar kasa in ji Aisha Abdussamad shugabar kwamitin kamfen Tinubu/Shettima a jihar Kano.

Aisha ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar Albishir makon da ya gabata ta ce, tabbas Tinubu jajirtaccen dan siyasa ne kuma mai hangen nesa idan har Allah ya sa ya zama shugaban kasa, Nijeriya za ta samu canji wanda ba’a taba samun irin sa ba domin sanin kowa ne cewa, Tinubu jajirtacce ne kuma mai son ci gaban al’umma musamman matasa maza da mata domin a lokacin da ya yi gwamna daga 1999 zuwa 2007 fiye da matasa dubu 100 mata da maza aka dauka aikin shara.

Wanda kuma ake biyan su dubu 30 duk wata domin rage zaman banza da rashin aikin yi a jihar Ikko kuma shi ne gwamna na farko da ya fara kawo hukumar rage cunkoso na ababen hawa a jihar Ikko kwatankwacin Karota a jihar Kano, domin haka zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa alheri ne ga ‘yan Nijeriya.

Shugabar matar ta ce, Nijeriya na bukatar jajirtacce mutum kuma gogagge kamar Bola Ahmed Tinubu wanda zai kawo ci gaba da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa da kuma kawo karshen rashin tsaro da ya addabi  Nijeriyamusamman Arewa domin haka ta yi kira ga al’ummar kasar nan da su zabi Bola Ahmed Tinubu bisa cancanta da kuma jajircewa.

Daga karshe, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su fito su yi katin zabe domin sai da kuri’a za ka nemi ‘yanci kuma ka zabi wanda kake so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *