‘Yan Nijeriya na bukatar agajin gaggawa -In ji Adamu Alhassan

Tura wannan Sakon

Shugaban kamfanin Simple 2 Tedtile da ke Kantin-kwari kuma matashin dan-kasuwa, Alhaji Adamu Alhassan Muhammad ya ce, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya musamman talakawa suke bukatar agajin gaggawa domin talauci ya sami gindin zama a kasar amu mai albarka.

Ya ce, hakika talauci shi ne babban kalubale da Nijeriya ke fuskanta a yau kuma babban barazana ga miliyoyin al’umma ‘yan Nijeriya a yanzu haka.

Matashin dan-kasuwar ya yi jawabin ne da yake ganawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano a satin da ya gabata ya ce, rashin aikin yi ga matasa rashin kwakkwarar sana’a ga al’umma da kuma uwa uba rashin tsaro ya sa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin tsaka mai wuya kuma ba zai haifar da da mai ido ba, kuma idan har tura ta kai bango babu shakka ‘yan Nijeriya da kansu za su nemi mafita wanda kuma ba haka aka so ba ya kamata a dubi lamarin da idon basira.

Muhammad ya kara da cewa, idan har ana son ci gaba a Nijeriya kuma da gaske ake lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya masu hannu da shuni da shugabanni da ‘yan-kasuwa da malamai da sauransu, a dawo turbar gaskiya da kuma son juna da kuma taimakekeniya a tsakanin al’umma domin shi zai bayar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

Alhaji Adamu ya ce, al’ummar Nijeriya na cikin kuncin rayuwa domin haka ya zama wajibi a tashi tsaye na ganin an kawar da kalubale da barazana ga al’umma.

Ya bayyana cewa, duk wanda ya taimaka shi ma Allah zai saukaka masa ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su yi amfani da lokacin watan Ramadan domin neman falala da kuma samun rahamar Ubangiji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *