‘Yan-siyasar Kano, yaya ne?

Shekarau, Ganduje da Kwankwaso
Kwamrad Ibrahim Abdu Zango
Ga alamun da muke ciki a jihar Kano, zamu fahimci cewa, ‘yan siyasar wannan lokacin sun kasa gane cewa kafinsu akwai wasu jarumai masu mutunci wadanda basu yi siyasa domin tara abin duniya ba.
Ga mutumin Kano wanda Allah Yasa ya sami wadancan mutane lokacin rayuwarsu yasan cewa mutane ne masu dattaku da kaunar jama’a cikin lokacin da suka sami kansu suna masu lura da bukatar talaka ya samun sukunin rayuwa cikakkiya wacce ake daukar mutum kamar bawa bayan Allah Ya halicce shi mutum mai ‘yanci kamar kowa.
Koda yake lokacin wancan zamani, akwai siyasu biyu wato NPC da NEPU kuma wadannan jam’iyyu biyu gaskiya kishiyoyin juna ne, kuma sun sha bambam wurin ra’ayoyi domin NPC ana ganin kamar ta ‘yan ra’ayin rikau ne, saboda akwai sarakuna wadanda suke tafiya tare da ita kuma NEPU itace mai rigima da hanyoyin da ake takurawa talakawa ta biyan haraji da sauran abubuwa na cuzgunawa.
Gaskiya koda yake bayan NPC ta gama mulkinta bayan anyi juyin mulki, amma da aka nutsu bayan gwamnatin NPC ta kau, sai aka fahimci cewa ashe dai arewa ta shiga uku saboda rashin wadancan manya da aka kwace mulki a gunsu ganin gina abubuwan kirki da gwamnati tayi cikin kankanin lokaci na shekaru shida kacal! Gwamnatin NPC ta ginawa arewa abubuwa da yawa na kyautatawa talakawa, kususan harkar noma, wadda duk wani talaka komai talaucinsa ya amfana kuma ‘yan boko masu karancin ilimi aka sama musu aiki ofis-ofis don su cike wurare da mutanen kudu suka bari domin komawa sansaninsu wato “Probinces” a turance, kuma anga babbar jami’a wacce akayi a Zaria wato wacce aka sa mata sunan Ahmadu Bello Unibersity (ABU) kenan.
Sannan aka kafa gidan jaridar New Nigeria da Radio Telebision Kaduna, kari da wata hukuma wacce ake kiranta a turance “Marketing Board” wacce take kayyade kayan saye da sayarwa wadda har gobe ana amfani da ita a dukkan kasashe masu ainahin cigaba.
Kai duk wani fanni na ili- mi ne, lafiya ne, tsaro ne da tattalin zamantakewa an same shi a waccan gwamnati ta NPC.
Kaga ashe dai shine aikin siyasa ba hauma-hauma ba, wacce yanzu muka gani wurin ‘yan dagajin siyasa wadanda kawai suke amfani da talakawa kuma suke tara kudin wuta balbal! To lokacin NPC dai akwai manya manyan jihar Kano kuma dasu aka sami cigaban da muke fadi kamarsu Alhaji Inuwa Wada Magajin Gari, Alhaji Sule Gaya da Alhaji Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano da dai sauransu, Allah Ya jikansu yasa Aljannah Firdausi suka koma, da iyayenmu ‘yan uwa musulmi gaba dayansu amin summa amin.
Malam Aminu Kano shugaban talakawa shine jigon tabbatar da wadannan ayyukan kirki da NPC tayi duk da yana NEPU domin suke zungurar NPC, adawa ta gari kaga haka siyasa take, amma bata kushe komai ba, kamar yadda ake taka leda a Kano.
Taka ledar siyasar jihar Kano ta zama ta kyashi da bakin ciki kuma siyasar ta kasance ta gidajen radiyo inda wasu jama’a suke shiga domin cin mutuncin mutane. Kuma wai a yau akwai wasu masu takama da Kano cewa su ‘yan wata siyasane wacce shugaba Buhari yayi wai ita CPC wacce a lokacinma jiha daya tilo taci wanda koda kansila basu ciba a Kanon tasu, sune fa suka cika Kano da yaransu cewa sune na kusa kusa da Buhari suke ta soki burutsu a yanzu na nakasta Gwamnan jihar Kano, wato Maigirma Dr. Abdullahi Umar Ganduje mutumin kirki mai hakurin gaske.
Abin mamaki wai har ire-iren wadannan mutane suna bugar kirji cewa, sune suke da fada a can Abuja kuma wai sai sunga bayan wannan gwamnatin da ta bawa shugaba Buhari goyon baya fiye da kima.
Allah Sarki ashe siyasa ba gaskiya, munafunci ne, ba wai gaskiya ce abar bida ba, sai ‘yan kamashonta ne kawai suke jin dadinta! To gaskiya dai itace su Malam Ibrahim Shekarau ai kowa ya sani ‘yan hamayya ne ga shugaba Buhari tunda ya tsayawa ANPP shugabanci, shi kuma Maigirma Buhari ya tsayawa CPC anan fa za’a gane cewa dawowar Shekarau APC yanzu duk da yana tutiyar cewa sune suka tsara kundin tafiyar da APC wannan baya nufin baiyi rawa ba, a siyasance, kuma yanzu labewa da yayi a bayan wai su Sanata Barau bata sake zani ba, domin babu yadda zata yiwa Kura da Damisa su sami sukunin zama rami guda, kuma ko su waye suka daurewa ‘yan tawaye bakwai gindi, babu yadda shi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai yarda ya bawa bori kai ya hau nakada ba.
Sanata Barau yasan Kwankwaso, Kwankwaso yasan abubuwan da Barau yayi masa tare da Ghali Umar Na’abba, Ganduje sha kuruminka tafiyar ‘yan bakwai ta kwabe musu, Allah Ya jikan Alhaji Bashir Othman Tofa, Allah Ya yafe masa kurakuransa, Yasa Aljannah Firdausi ce makomarsa, Amin. Naku Kwamrad Ibrahim Abdu Zango Chairman: Kano Unity Forum, Kano – Nigeria, 08175472298