‘Yan-ta’adda sun farmaki Buni Yadi-Sun Kona ofishin ‘yan-sanda, firamare

‘Yan-ta’adda sun farmaki Buni Yadi

‘Yan-ta’adda sun farmaki Buni Yadi

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

Wadansu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne vangaren ISWAP sun kai hari garin Buni Yadi karamar hukumar Gujba, jihar Yobe.

Wakilinmu ya rawaito cewa ‘yan-ta’addar sun kona ofishin ‘yan-sanda da makarantar firamare. Wani daga cikin mazauna garin na Buni Yadi wanda ya nemi a voye sunansa, ya bayyana wa wakilinmu ta wayar tafida-gidanka cewa, maharan sun shigo garin wajen karfe 5 na yamma tare da yawan gaske dauke da makamai cikin motoci kirar Toyota Hilud a-kori-kura.

Malamin ya kara da cewa, shigowarsu garin ke da wuya kawai sai suka rika harbe-harbe ta ko’ina kamar yadda suke yi yayin da suka kawo hare-hare wadda jin haka ya sa mutanen garin cikin halin firgici da razana tare da kokarin neman wajen vuya domin tsira da rai.

Kamar yadda ya ce, “da yawa-yawanmu da muka sami tserewa zuwa cikin daji mun yi ta jin karar harbe-harben manyan makaman yaki wadanda Daga shafi na farko Wannan yarinyya vata ta yi, a taimaka mana da cigiya. Sunanta Fatsima. A Naibawa ‘Yan Lemo gidansu yake.

Ga lambar mahifinta Abubakar Mustapha 08067213986. bisa ga dukkannin alamu makaman jami’an tsaron soja ne da ke garin, hakan ya sa muka kara yin gaba.”

Wata majiya daga garin ta sake tabbatar wa wakilinmu cewa, ana cikin hakan ne sai ga dauki daga mashahurin jirgin yakin nan na dakarun sojan sama samfurin Tukano ya zo, ya rika harba wa wadannan ‘yan bindiga manyan bamabama wanda hakan ya sa nan da nan ‘yan bindigar arcewa tare da barin makaman su domin tsira.

Shi ma wani magidanci da ya nemi a voye sunansa ya tabbatar da cewa, “lallai an kawo mana hari a garinmu duk da dimbin jami’an sojan da ke kewaye da mu amma kuma sai da wadannan shu’uman ‘yan bindiga suka shigo garin wanda a yanzu haka ni ma an kona min gidana.”

A Cewarsa, “hakan ya sa ba mu yi wata-wata ba da jin zuwan su ba mu yi kasa a gwiwa ba muka ranta a na kare kasancewar, Hausawa kan ce ruwan da ya dake ka shi ne ruwa, domin a baya sai da muka gudu muka bar garinmu muna ji muna gani daga bisani ne jami’an tsaron kasar nan suka sake kwato garin har muka samu muka dawo.”

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Yobe, Abdulkarim Dungus da manema labarai suka tuntuve shi kan faruwar harin ya ce, zuwa yanzu rahoton hakan bai iso gare su ba amma da zarar ya samu zai sanar da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *