‘Yan-ta’adda sun fi mu makamai, mun fi su jarumtaka -Bazoum

‘Yan-ta’adda sun fi mu makamai, mun fi su jarumtaka -Bazoum

Shugaban Kasar Nijar Bazoum

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mohamed Bazoum ya ce, makaman da ‘yan-ta’adda suke amfani da su domin kai hari a kasarsa da yankin Sahel, sun fi na sojojinsu.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taro na duniya kan zaman lafiya da tsaro da aka gudanar a Dakar babban birnin Senegal.

Ya koka kan yadda masu ikirarin jihadin ke ci gaba da kara karfi a kasarsa da ma yammacin Afrika.

Ya ce, babu wani wuri a duniya da ‘yan bindiga suka tava samun irin makaman da jami’an tsaron da ke yaki da suke amfani da su, amma ga shi a yau hakan na faruwa a yankin Sahel. .

Shugaban, ya bayyana cewa, sojojin kasashen Yammacin Afirka na bukatar sababbin dabaru domin yakar masu ikirarin jihadin da ke kara karfi sakamakon yalwatar fasahohin zamani ta kara bai wa ‘yan bindigar wata dama a daidai lokacin da suke kokarin lalata yankin Sahel.

Yankin Sahel wuri ne da masu ikirarin jihdi suke kara zafafa kai hare-hare da kashe dubban mutane da kuma raba miliyoyi da muhallansu, in ji shi.

Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Kaeda da IS kamar su Boko Haram da ISWAP sun kara fadada a tsakiyar yankin na Sahel tun daga shekara ta 2017 tare da kaddamar da hare-hare a Mali da Nijar da Burkina Faso da Nijeriya.

Hare-haren da aka kai na baya-bayan nan a Nijar a karshen makon jiya, shi ne wanda ‘yan bindiga suka kashe akalla sojoji 12 yayin wata arangama a kudu maso yammacin iyakar kasar da Burkina Faso.

Ko a watan Nuwamba sai da gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu bayan da wadansu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne suka kashe mutane 70.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *