Yanayin siyasa: Tinubu, Kwankwaso sun yi tozali a Faransa

Tura wannan Sakon

Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a kasar Faransa.

Shugabannin biyu sun gana a birnin Paris babban birnin Faransa, inda rahotanni ke cewa, sun tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar gabanin kaddamar da babban taron kasa karo na 10 a ranar 13 ga Yuni.

Rahotanni sun ce, Tinubu ya bar kasar ne a ranar Laraba 10 ga Mayu, 2023 zuwa Turai. Zababben shugaban kasar ya shaida wa Kwankwaso cewa, ya tuntubi abokan siyasarsa kan bukatar yin aiki tare.

An ce shugaban mai jiran gado da bakon nasa sun amince da gudanar da tarurruka game da ci gaban kasar. Yayin da uwargidan Kwankwaso da Abdulmimin Jibrin, zababben dan majalisar wakilai na NNPP, Alhaji Abdulmini Jibrin Kofa suka raka shi wurin taron, uwargidan Tinubu da Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai mai barin gado, na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Zababben shugaban kasar da Sanata Kwankwaso sun yi ganawar fiye da sa’o’i 4 a birnin Paris ranar Litinin. Majiyar ta ce, Tinubu ya kuma yi tsokaci kan sasanta gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Sanata Kwankwaso.

A shekarar 2015 ne Ganduje ya gaji Kwankwaso, amma ba da dadewa ba suka samu sabani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *