Yawaitar tallace-tallace kan kayyade iyali: Majalisar Malamai ta nuna wa kafafen yada labarai yatsa

Rikicin Malaman Kano: Imam Alhamidi ya yi gum

Sheikh Ibrahim Khalil

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Majalisar Malamai ta jihar Kano ta damu sosai da yawaitar tallace-tallace a kafafen yada labarai a kan tsarin kayyade iyali da sunan tsarin bayar da tazarar haihuwa.

A wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun shugaban Majalisar, Sheikh Ibrahim Khalil ta nuna cewa, wadansu daga cikin membobin Majalisar sun bayar da sanarwa bisa karuwar korafe-korafe daga al’umma kan batun.

 Kasancewar al’umma ta damu sosai bisa abin da tallace-tallacen za su haifar ta wajen tarbiyya da kuma damar da suke da ita ta kula da  ’ya’yayensu.

“A fahimtarmu, abin da ya shafi tsarin bayar da tazarar haihuwa, abu ne da ya shafi ma’aurata su kadai sai kuma likitan da suka tuntuba” a ta bakin Majalisar.

 “Saboda haka,  mafiya rinjayen malamai, sun tafi a kan cewa, bai kamata a fito fili ana tallata tsarin ba, saboda yin hakan zai haifar da cutarwa fiye da amfani ga al’umma. A bisa wannan dalilin, ya haramta a bangaren Shari’a, ma’ana, tallace-tallacen” cewar bayanin.

Saboda tsananin damuwar Majalisar da kuma al’umma baki daya, muka ga yana da muhimmanci mu rubuta da kuma tambayar hikimar daukar shawarar yin tallace-tallace marasa kyau a cikin al’ummar Musulmi.

A karshe majalisar ta nusar da cewa, idan kafar yada labaranku tana cikin masu tallata mummunar akidar, karin  bayaninku lallai zai mutukar taimaka mana ta yadda za mu fuskanci al’umarmu da wadanda suka yi mana tambayoyi a kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *