Yi wa Fursunoni 236 Afuwa: Kanawa sun jinjina wa Ganduje

Ganduje ya yi wa Fursunoni 236 Afuwa

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

A duk lokacin da ake gu­danar da wata hidima ta bukukuwa ko shagulgu­la da suka shafi zagayowar wata rana da ake murna shugabanni sukan yiwa wasu daga cikin fur­sunoni afuwar laifukan da suka aikata har ta kai su ga shiga gi­dajen gyaran hali.

Hakan yana kara taimaka wa wajen kyautata halayyar al’umma musamman masu ai­kata laifuffuka tare da mayar da su mutane na kwarai bayan kammala zaman gidajen gyaran hali koda kuwa an yanke masu hukunce-hukunce daidai laifu­kan da suka aikata.

Bisa wadannan dalilai ne, gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa wadansu fursunoni 136 afu­wa daidai lokacin da ake tsaka da shagulgulan Babbar Sallah, wanda hakan ya sa al’ummar jihar Kano dama sauran mutane da ke wadansu jihohi suka yi godiya da fatan alheri ga gwa­man da kuma gwamnatinsa.

Mafiya yawan mutanen da suka zanta da wakilinmu sun bayyana wannan abin kirki da gwamna Abdullahi Umar Gan­duje ya yi ya nunar da cewa, shi shugaba ne adali kuma mai kau­nar ganin al’umma cikin yanayi mai kyau duk da cewa, doka ta bayar da damar yin hukunci ga dukkanin wadanda suka yi laifuffuka a tsakanin al’umma.

Sannan sun nunar da cewa, yi wa daurarre afuwa abu ne mai kyau domin wadansu suna zamowa mutanen kirki domin haka abin da gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi abu ne da yake yi wa kowa dadi, saboda dukkanin wanda ya bai wa dan’adam yancin da to ya yi abin da ya ka­mata.

Ustaz Usman Dan Almajiri, wani malami mai bayar da fata­wa da ke Kano ya ce “ a duk lo­kacin da wani mutum ya fitar da bayin Allah daga wani kangi ko shakka babu ya yi abin da Allah ke so, sannan su kansu wadanda aka fitar din zasu iya kasancewa mutanen kirki a cikin al’umma, domin haka muna yi wa gwam­na godiya tare da fatan alheri ga gwamnatinsa”. In ji Ustaz Us­man.

A karshe, dukkanin wadanda suka yi magana da Albishir sun yi horo ga fursunonin da shuga­banni ke yi wa Afuwa da su ci gaba da kasancewa mutane na­gari masu kaunar zaman lafiya da karuwar arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *